MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: KUNGIYAR CAN ZATA SHIRYA MUHAWARA TSAKANIN BUHARI DA ATIKU 10 GA WATAN DISAMBA-Karanta Kaji Dalili

Kungiyar CAN Ta Kasa Zata Shirya Muhawara Tsakanin Buhari Da Atiku-Karanta Kaji Dalili

A kokarinta na inganta yakin neman zaben shekarar 2019 don ta karkata wajen tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin yan Najeriya ba wai cece kuce, zagin juna da cin zarafin juna ba, kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, za ta shirya muhawara tsakanin yan takarar shugaban kasar Najeriya.

Majiyar Mujallarmu.Com ta ruwaito cewa hukumar CAN za ta shirya muhawarar ne tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta, Legacy Initiative International, kamar yadda shugaban kungiyar, Kenny Martins ya bayyana.

Mista Kenny Martins ya bayyana haka ne a ranar Talata 4 ga watan Disamba yayin da yake ganawa da manema labaru a jahar Legas, wanda yace sun shirya mahawarar ne da hadin gwiwar CAN don tabbatar da an tattauna abubuwan da suka shafi yan Najeriya.

A cewar Martins, sun shirya mika al’amuran zaben shekarar 2019 ga ubangiji Allah ne, don haka zasu fara da gudanar da taron addu’o’I daga ranar 10 ga watan Janairu a karkashin jagorancin shugaban CAN, Supo Ayokunle.

“Haka zalika shirye shirye sun yi nisa tsakanin da yan uwanmu Musulmai don gabatar da addu’o’i a babban birnin tarayya Abuja da kuma jahar Legas, manufar hakanshine don wayar da kawunan dukkanin yan Najeriya ga cewa duk abinda ya faru a zaben 2019 yin Allah ne.” Inji shi. Daga karshe Martinsa yace suna addu’ar Allah ya dawwamar da zaman lafiya da cigaba mai daurewa a Najeriya daga yanzu har zuwa zaben shekarar 2019, da ma har bayan zaben 2019.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-12-05 — 10:48 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme