MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: INA MAMAKIN YADDA JAM’IYYAR APC KE SAYEN KATIN ZABE A HANNUN JAMA’A AKAN FARASHIN NAIRA 10 NAIRA 20-Inji Atiku

       Ina Mamakin Yadda APC Ke Sayen Katin Zabe A Hannun Jama’a

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a yau Laraba, 5 ga watan Disamba, 2018 a taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP da aka gudanar a Ilori, jihar Kwara.

Yace: “A yau, mun ji gazawar gwamnatin APC daga shekarar 2015 zuwa yanzu. Babu irin alkawarin da basu yi mana ba, sunyi alkawarin tsaro, samar da ayyukan yi, karfin tattalin arziki, kuma duk sun fadi.”

“Lokaci yayi domin mayar da Najeriya hannun PDP, saboda shekaru mafi albarka a tarihin kasar nan lokacin da PDP ke mulki tsakanin 199 da 2015 ne.”

“A bangaren rashawa kuwa, abin ya fi tsanani a Najeriya fiye da shekarar 2014.” “Abinda APC ke yi shine. Suna saya katin neman zabe PVC. Za su zo wajenku suna baku N10, N20, N50 domin sayan katinku. Sun sayan rana gobenku ne.Har yanzu, kakakin jam’iyyar APC bai mayar da martani kan wannan zargi ba.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-12-06 — 2:17 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme