MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: Hukumar INEC Ta Bayyana Cewa Anyi Lalata Da Jami’anta Mata Lokacin Zaben Shugaban Kasa Da Aka Gudanar Satin Daya Gabata

Wata-sabuwa: An yi zina da ma’aikatan mu lokacin zaben shugaban kasa -Inji INEC

Hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commisslon (INEC) ta bada labarin cewa an yi zina da wasu ma’aikatan ta mata a yayin zabukan da aka gudanar satin da ya gabata na shugaban kasa da ‘yan majalisar wakilai.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban jami’in yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar Mista Festus Okoye ya fitar dauke da sa hannun sa.

A cikin sanarwar, Mista Festus Okoye ya bayyana cewa duk da dai zaben da aka gudanar a iya cewa an yi shi ne cikin lumana a dukkan fadin kasar, amma dai hukumar ta dan samu tsaiko a wasu wuraren yayin zaben.

Ya ciga da cewa hukumar ta Independent National Electoral Commisslon (INEC) ta samu labarin tashe-tashen hankula da satar mutane da yiwa jami’an su fyade da ma rasa rai a wasu wuraren.

Haka zalika Mista Festus ya kuma yi anfani da damar wajen jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukan su ko jikkata koma rasa dukiya a wasu wuraren tare da basu hakuri da kuma tabbacin karin matakan tsaro daga hukumar domin kaucewa kara aukuwar lamarin a gaba.

 

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-03-01 — 8:01 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme