MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WATA SABUWA: Ana Zargin Dan Kwallon Kafa Na Duniya Cristiano Ronaldo Kan Lafin Fyade-Karanta Kaji

      Rundunar ‘yan sanda ta bukaci gwajin jinin Cristiano Ronaldo kan zargin fyade

Rundunar ‘yan sanda ta Las Vegas ta bukaci shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo da ya gabatar mata da gwajin jinisa

Bukatar gwajin jinin nasa ya biyo bayan wani zargi da ake yi masa na yiwa wata tsohuwar mai tallace tallace fyade a shekarar 2009.

Kathryn Mayorga tayi ikirarin cewa Ronaldo ya yi mata fyade a dakinsa da ya kama a wani otel a ranar 13 ga watan Yuni 2009, kafin ya fara buga wasa a Real Madrid Rundunar ‘yan sanda ta Las Vegas ta bukaci shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo da ya gabatar mata da gwajin jinisa, a cikin binciken da take gan gudanarwa na zargin da ake yi masa na aikata laifin fyade.

Dan wasan gaba na Juventus ya karyata wannan zargi da ake yi masa, ta bakin lauyansa, Peter Christiansen, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, cewar wannan bukatar na da tsauri.

“Mr Ronaldo na da taka tsantsan a kullum, kamar yadda yayi a yanzu, abun da ya faru a Las Vegas a 2009 wani lamarine na kaddarar rayuwa, don haka ba zai zama abun mamaki don an bukaci gwajin jininsa ba, amma bamu yi tunanin cewa rundunar ‘yan sandan zata gabatar da wannan bukatar a yanzu ba,” ya ce a cikin wata sanarwa.

Rundunar ‘yan sanda ta Las Vegas ta ce ta gabatar da wannan bukatar ne ga hukumomin Italia, inda ta kara da cewa “daukar wannan matakin ba wai a kansa kadai bane, ya dogara ne akan duk wani da ake zarginsa da yin fyade, dole ne a bukaci gwajin jininsa.

” Tsohuwar yar tallace tallace, Kathryn Mayorga, mai shekaru 34, da ke da zama a Las Vegas, ta zargi Ronalad da yi mata fyade, a wani korafi da ta shigar karshen shekarar data gabata a garin Nevada.

Ta yi ikirarin cewa bayan haduwarta da shi a wani dakin rawar dare a Las Vegas, ya yi mata fyade a dakinsa da ya kama a wani otel a ranar 13 ga watan Yuni 2009, kafin ya fara buga wasa a Real Madrid, bayan barinsa Manchester United. Mayorga ta yi ikirarin cewa an biyata $375,000 domin ta yi shiru da bakinta kan wannan lamari.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-12 — 12:38 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme