MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Wata Mata ta nemi mijinta ya saketa don tsananin son da yake mata.

Wani matashi dan shekara 29 a kasar Saudia ya sami kanshi cikin matsanancin rudani yayin da matarsa wadda yafi kauna daso fiye da kowa ta kaishi kotu don a raba su. Wannan mijin yayi mamakin yadda matarshi ta nemi ya saukaka mata igiyar auren su ya sake ta duk da kokarin da yake mata wajen kyautatawa.

Amma matar ta nuna da gaske take sai fa ya sake ta, ta kuma tabbatar da cewa bata taba rasa samun biyan bukata ta duk wani abu da take so daga gare shi, amma ta matsa lalle sai ya sake ta saboda ya fifitata fiye da mahaifiyar shi. Da alkali ya tambayeta dalilin neman sakin sai tace bazan taba amincewa mutumin da yake ma matarsa komai na kyautatawa, amma bai damu da hakkin mahaifiyar shi ba ko kadan baya kyautatama mahaifiyar shi.

Mijin wanda yake cikin rudani yace ma Alkalin shi baya so ya saki matarshi ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma zai iya yin komai don suci gaba da aurensu, amma Matar ta rufe idonta ta kekasa kasa tace bata yarda ba sai ya sake ta, matar ta tabbatar da cewa lalle kam mijinta yana mata dawainiya, yana kashe mata kudi masu yawa wajen fita da ita kasashen waje don yawon shan iska ya kuma saya mata duk abinda take so, amma bata so taci gaba da rayuwa dashi.

Tace mutumin da bai kyautatawa mahaifiyar shi bai kamata in aminta dashi ba, zai iya juyamin baya nan gaba a rayuwa, mijin ya tambayeta cikin mamaki ban rabu da dangina da yan’uwana saboda ke ba? Tace kwarai shine ma dalilin daya sa nake so ka sake ni. Matar ta sheda ma alkali duk abinda mijin ta ya fada gaskiya ne amma ta yanke shawaran rabuwa da shi ne don ya fifitata akan yan’uwan shi da danginsa harma mahaifiyar shi, tace ma Alkalin bazata jira har ranar da itama zai juya mata baya kamar yadda ya butulce ma mahaifiyar shi ya juya mata baya.Matar ta dawo ma da mijin sadakinsa Alkali ya bada sakin
Wani mai sharia ya yaba ma matar ganin jarumtar ta yace tayi gaskiya data nemi saki daga mijin daya fifita mata akan mahaifiya shi, yace matar tayi tunanin mutumin da zai iya rabuwa da mahaifiya don wata mace bai cancanci a gaskata shi ba. Wasu mazan sun dauka yima mace biyayya ido rufe kesa samun nasaran soyayyan macen, amma kash ba haka bane dole ne mutum ya karrama mahaifiyar shi fiye da kowa. Yace matar bata jin dadin hidimar da yake mata don ya fifitata fiye da matar data haifo shi ta rene shi ta sadaukar da rayuwarta don farin cikin shi
(c)okaz/saudi Gazette (anti Dada )

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2018-01-07 — 11:06 am

2 Comments

Add a Comment
  1. hakika tayi gaskiya komai mai iyafaruwane!!

  2. Allah yahadata da wanda ya fishi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme