WASANNI: YANZU NA JANYE KUDIRI NA ZUWA BARCELONA SABODA MESSI REAL MADRID ZAN KOMA-Inji Paulo Dybala

Na Janye Kudirina Na Zuwa Barcelona Saboda Messi-Inji Paulo Dybala.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shahararren dan kwallon kafa dake dake taka leda a kulob din Juventus Paulo Dybala yace ya janye kudirin sa na zuwa kulob din Barcelona dake kasar Spain saboda Messi.

Kamar yadda majiyar ta Dandalin Mujallarmu,keda labari messi ya bukaci mai kulob din na Barcelona daya sawo Paulo Dybala daga Juventus,saboda ya maye tsohon dan wasan su da yabar Barcelona Neymar dake buga kwallo yanzu a kulob din Paris Siant German PSG.

Sai dai kuma a wani Rahoton alamu sun nuwa cewa mai kulob din na Juventus ya sanya makudan kudade akan dan wasan kimamin Euro miliyan 131  darajar kudin kasar Italy.

Abisa jawabin da Messi yayi da mai kulob din na Barcelona,ya bashi shawara akan cewa kada ya bata makudan kudaden sa a banza wajen sawo Paulo Dybala ,tunda baida ra’ayin buga wasa dashi a kulob din na Barcelona.

yanzu haka dai Paulo Dybala yace Kulob din Real Madrid yake da burin taka leda a kakar bana,kuma duk yayi hakane saboda Messi da suke kasa guda Argentina.

This website uses cookies.