MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WASANNI: SAI ALBASHI NA YAKAI FAM DUBU DARI HUDU SANNAN ZAN KOMA MANCHESTER UNITED-Inji Griezman

Ina Bukatar Albashina Yakai  Fam Dubu Dari Hudu Kafin Na Fara Buga Wasa A Manchester aUnited-Inji Antoine Griezman. 

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Antoine Griezman, dan kasar faransa ya bayyana cewa idan har Manchester United zasu bashi albashin fan dubu dari hudu a shirye yake daya koma kungiyar.
Griezman, mai shekara 26 a duniya yakusa komawa Manchester United a kasuwar siye da siyar da yan wasan data gabata kafin daga bisani ya canja shawara bayan da aka cigaba da dakatar da kungiyarsa ta Atletico Madrid na hanata siyan yan wasa sakamkon laifin da sukayi na siyan kananan yan wasa.

Sakmakon hakane kungiyar Manchester United taje ta biya fam miliyan 75 ta siyi Rumelu Lukaku daga kungiyar kwallon kafa ta Eberton sai dai watakila kungiyar ta koma zawarcin dan wasan a wannan watan na janairu sakamkon kungiyar ta Atletico ta siyi tsohon dan wasan Chelsea, Diego Costa.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona itama tana zawarcin dan wasan amma sakamakon siyan dan wasa Coutinho da kungiyar tayi wata kila ta hakura da dan wasan domin ta kasha kusan fam miliyan 146 akan Coutinho.

An bayyana cewa shima Griezman din yana fatan cigaba da zama a kasar sipaniya sai dai watakila dole idan har yanason barin Atletico Madrid dole sai yabar kasar ta sipaniya domin zuwa wata kasar daban.

Manchester United dai zata yimasa tayin albashin fan dubu dari biyu da casa’in sai dai dan wasan zaiso sama da haka sakamakon yadda yan wasa suke tsada a yanzu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-01-12 — 12:42 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme