MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

WARWARE ZARE DA ABAWA: GASKIYAR ZANCE

Akwai wani labari mai daukan hankula dake yawo a kafafen sadarwa na zamani wato ‘social media’ akan wani batu na cewa Mai Girma Gwamnan Jahar Bauchi Mohammed Abubakar zai bayyana a cikin wani shirin fim. Wasu da dama sun fahimci lamarin har suna fatan alheri, sannan akwai wasu tsiraru kuma da suka kasa fahimtar yadda zancen yake. Tabbas ko kadan bama zarginsu, hasali ma mun sani kuma mun yarda cewa ko wani dan kasa yana da ‘yancin fahimta da kuma fadan albarkacin baki. Amma duk da haka, yana da kyau idan zaka fadi, ka fadi gaskia.

muhammad abubakar bauchi governor

Wannan fim dai da ake magana akai sunan shi ‘Up North’. Fim ne wanda babban mai bada umarnin nan wato Tope Oshin ta bada umarni sannan manya-manyan jaruman fina-finan Najeriya irinsu Banky W, Kanayo O Kanayo, Hilda Dokubo, Rahma Sadau, Ibrahim Onimisi-Suleiman da kuma shahararren mai wasan barkwancin nan wato Funky Mallam.

Wannan fim, wanda kamfanin Anakle tare da hadin gwiwa da kamfanin Inkbolt suka shirya, ya taba fannoni da dama wanda mafi girma daga ciki shine mahimmancin karatun ‘ya mace da kuma hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya. An dauki shirin wannan fim ne a Jahar Lagos da kuma Jahar Bauchi. Dalilin da yasa wadannan kamfanoni suka ga dacewar Bauchi a matsayin inda zasu dauki wannan shiri shine; 1.) Gwamnan Jahar Bauchi shine gwamnan da yayi fice a Najeriya wurin inganta harkar ilimi a Jaharsa musamman ma karatun ‘ya mace. 2.) Jahar Bauchi tana da wurare da dama na yawon bude ido masu daukan hankali kamar su gandun dajin Yankari, Sumu Park, dutsen Mbula dake karamar hukumar Dass da dai sauransu. Saboda haka daukar fim din a Bauchi zai kara armashi wa fim din sannan kuma Jahar Bauchi zata cigaba da tallatuwa a idon duniya kamar yadda Mai Girma Gwamna yake yi ba dare, ba rana kuma ko shakka babu hakan zai jawo wa Jahar Bauchi kudin shiga mai yawa.

http://mujallarmu.com/labarai/majalisa-ta-daukaka-kara-kan-hukuncin-canja-ranar-zaben-shugaban-kasa/

Game da bayyanar Mai Girma Gwamna a cikin wannan shiri kuwa ko kadan ba yadda wasu suke tunani bane. Kamar yadda na sanar daku a baya, wannan fim ya karkata ne sosai akan karatu, neman ilimi, hadin kan kasa da sauransu. Akwai wani scene guda daya tak da ake bukatar Gwamnan Jahar yayi jawabi ga ‘yan wata makarantar mata a yayin da zasu fara wata gasa a makarantar tasu. Hakan yasa masu shirin wannan fim suka roki Mai Girma Gwamna ya bayyana a matsayin shi na gwamna kuma yayi wannan jawabin mai ratsa zuciya ga ilahirin daliban domin karfafa musu gwiwa da sauransu. Hakan zai kara karfafa girman fim din, daukaka Jahar Bauchi a idon duniya, nuna wa duniya irin yadda Jahar Bauchi take da arziki daban daban, nuna yadda zaman lafiya da son juna ta wanzu a Jahar ta Bauchi (sabanin yadda da yawa suke zato), nuna yadda jama’ar Jahar Bauchi suke son baki da mutunta su.

A cikin wannan shiri an nuna yadda ake hawan Sallah, an nuna Mai Martaba Sarkin Bauchi da fadarsa mai dimbin tarihi, an nuna makwancin firayim minista na farko (kuma na karshe) a Najeriya, an nuna makarantar mata ta Kafin Madaki, an nuna gandun dajin Yankari da sauran wurare da dama. Wani babban abin sha’awa da kuma burgewa shine yadda matasa da dama ‘yan asalin Jahar Bauchi suka samu ayyuka daban-daban yayin shirin fim din; wannan nasara ce babba.

Ina ganin wannan babban abun alfahari ne ga ilahirin ‘yan Jahar Bauchi ba abin cece-kuce ba domin babu wani dalili na hakan.

Shamsuddeen Lukman Abubakar
Mataimaki na musamman ga Mai Girma Gwamnan Jahar Bauchi a fannin sadarwa

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-06-30 — 10:37 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme