MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

TSOHON GWAMNA BAFARAWA YA GOYI BAYAN EL’RUFA’I AKAN BUHARI

Tsohon gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce shi bai ga laifin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufa’i ya yi ba saboda ya rubuta wa shugaba Buhari wasikar gyara kayanka.

A baya-bayan nan ne dai wata wasikar da Nasir Elrufa’i ya rubuta wa shugaban Muhammadu Buhari, a watan Satumbar 2016, ta bayyana.

A cikin wasikar, Elrufa’i ya nemi shugaba Buhari da ya yi karatun tanutsu wajen aiwatar da ayyukan alherin da jam’iyyar APC ta alkawarta wa al’ummar Najeriya.

Duk da wannan wasikar ta haifar da kace-nace a kasar, a inda wasu ma ke ganin beken Elrufa’i, shi kuwa Alhaji Bafarwa ya ce sam gwamnan na Kaduna ba shi da laifi.

Attahiru Bafarawa ya kuma kara da cewa tun da jam’iyyar PDP ta gaza, ya kamata ace APC mai mulki ta fitar da ‘yan Najeriya daga halin da suke ciki.

Ga dai yadda hirar Attahiru Bafarawan ta kasance da Yusuf Tijjani.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-03-22 — 8:23 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme