MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

TONAN SILILI: Jaruma Fati Shu’uma Ta Bayyana Abinda Jarumi Adam Zango Yayi Mata Da Bazata Taba Mantawa Ba Arayuwarta-Karanta Kaji

Karanta Kaji: Fati Shu’uma Ta Bayyana Abinda Adam Zango Yayi Mata Arayuwarta.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Fitacciyar jarumar fina finan hausa wadda take sahun farko acikin jerin sunayen matan kannywood da tauraruwar ke haskawa wadda akafi sani da Fati Shu’uma ta fito ta bayyana abinda jarumi Adam Zango yayi mata na alkhairi a rayuwarta wanda bazata taba mantawa dashi ba.

Fitacciyar jarumar dai ta bayyana hakane acikin wani gajeren bidiyon data sanya akan shafinta na instagram inda tayi wani takaitaccen jawabi da jinjinawa ga jarumi  Adam Zango ga abinda tace acikin bidiyon

“ Da farko dai jarumar ta fara da sallama tace Assalamu’alaikum mai gidana Adam Zango,jarumar tace naga kayi posting shine nace to bari na fadi alkhairan da kayi min a rayuwata.

Allah ne sanadi kai sanadiyya kai min film duniya ta sanni,jama’a suka sanni saboda haka ina alfahari dakai bisa wannan kokari naka,kuma ina alfahari da abinda kayi min bazan taba mantawa ba a rayuwata.

Sannan akwai wani abu da kayi min wanda shine abu mafi girma da bazan taba mantawa dashi ba arayuwa taba,alokacin da mahaifiyata wadda haifeni ta rasu kazo min ka zauna a wajen zaman makoki,kasan kuwa cewa ba karamin dadi naji ba da wannan abin da kayii min.

yan uwana da yawa suma sunji dadin wannan abu da kayi nima kaina naji dadi,toh kaga kuwa tabbas bazan taba mantawa dakai ba da kuma irin alkhairin da kayi min ,kayi min rana saboda haka bazan iya boyewa ba har ace nakasa bayyana shi ba.

Yazama dole na fada domin kuwa ka taimake ni arayuwata,saboda dalilin film din da kayi min jama’a da dama suka sanni sannan kuma duk wanda yasan ni yasan ni ne da Fati saina auri zango kuma shine film wanda ya daukaka ni a duniya har na kawo matakin da nake a yanzu,saboda haka dole ace da mijin iya baba.”

Wannan dai shine abinda jarumi Adam Zango yayiwa jaruma Fati Shu’uma na alkhairi dayasa har tayi furucin cewa bazata taba iya mantawa dashi ba a rayuwarta.

Ku Cigaba Da bibiyar shafin Mujallarmu.Com Domin Samun Labaran Kannywood Da Duminsu.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-22 — 6:43 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme