MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

TOFA: ANYI KIRA GA KUNGIYOYI MASU ZAMAN KANSU DAKE KARE HAKKIN BIL’ADAMA DASU TURSASAWA GWAMNATIN NAJERIYA TA SAKI EL’ZAKZAKY

An Yi Kira Ga Jama’a, Kungiyoyi, Gwamnatoci Su Tursasawa Najeriya Sakin Sheikh Zakzaky

10/1/2018
Rahoton Auwal M Kura

Rubutawar Abdulmumini Giwa


An yi kira ga kungiyoyin masu zaman kansu, masu rajin kare hakkin bil adama da kuma gwamnatocin kasashe da su tursasawa gwanatin Najeriya da ta gaggauta sakin Sheikh Ibraheem Zakzaky domin ya samu daman kula da lafiyarsa. Shugaban Resource Forum ne na kasa Farfesa Abdullahi Danladi yayi wannan kira a wani taron manema labarai na musamman da aka gudanar a garin Kaduna a ranan laraba.

Ya bayyanawa manema labaran cewa labarin tsanantan yanayin jikin Sheikh Zakzaky ya bayyana ne bayan wani ziyara da na kusa da shi suka kai masa, inda suka bayyana cewa muryarsa ta yi kasa, jikinsa yayi rauni sosai kuma sashen jikinsa na dama baya aiki yadda ya kamata.

Malamin ya kasance a wannan yanayi tun kwanaki bakwai da suka gabata daga ranan da aka yi wannan taron.

Ya kuma kara da cewa dama Shehin Malamin na fama da hawan jini kusan yanzu shekaru goma kenan inda hana masa daman ganin kwararrun likitocin da zasu kula da lafiyarsa da gwamnatin Muhammadu Buhari tayi ya munana lamarin. Farfesan ya bayyana cewa a lokacin mummunan harin da sojoji Najeriya suka kaiwa Sheihin Malamin a gidansa da ke Zaria a watan 12 na shekara 2015, sun zazzage harsasun bindigoginsu a jikin dattijon da dan shekaru 67 yanzu wanda har ya sa ya rasa idonsa na hagu ya kuma samu rauni a idon dama.

Wani likitan ido na gwamnati da ya duba shi ya bayyana cewa idon nasa na dama na bukatan kula daga kwararru kuma babu asibitin da zai iya yin wannan aiki a kasannan.

Ya kara da cewa hatta likitan da na kusa da Malam suka shirya ya duba jikin nasa, hukuman tsaron na DSS dake tsare da shi sun hana likitan ya gan shi.

Yanayin jikin Malam dai ya tsananta sosai ta yadda a zaune ma yake zama yana sallah kuma gwamnati ta hana a kula da lafiyansa kuma ta ki kula da lafiyan malamin duk da cewa Malam ne ke ciyar da kansa, yake biyan kudin wutansa da sayan mai da ake sanya wa janareta da duk sauran bukatunsa duk da cewa su ke tsare da shi.

Malamin Jami’an ya kara da cewa mai dakin Shehin Malamin, Malama Zeenatu Ibrahim ma na dauke da harsasu da sojoji suka harbeta a lokacin harin da suka kai musu a jikinta. Amma duk da ciwon da take fama da shi sun ki bata daman ta samu kula daga likita domin a cire mata su.

Da ga karshe dai ya bayyana cewa almajiran ShehK Zakzaky sun dauki matakai na hankali wurin ganin cewa an saki jagoransu inda suka shigar da kara kotu kuma kotu ta ba da umarnin a sake shi amma gwamnatin Buhari ta yi burus da wannan umarni.

Ya kara da cewa kuma almajiran suna gudanar da zanga-zangan lumana domin kira ga a saki jagoransu amma gwamnatin sai ta turo yan sanda su bisu da harbi da kisa inda ko a ranar lahadi da ya gabata sun kashe mutum biyu a garin Kaduna kuma suka kama sama da mutane dari a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Yace wadannan duka sun saba wa sashe na 35 na dokokin Najeriya da suke kari hakkokin bil adama da kuma sashe 6 na yarjejeniyar kare hakkokin bi adama na Afirka. `

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-01-10 — 3:27 pm

3 Comments

Add a Comment
  1. Usman Sani Gwarzo

    Allah ya daidaita al’amuran amin.

  2. Wannan govnati baby mutunchi atare da ita

    1. HMMM abidai ahankali,gaggawabayatuka tuwon makaho.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme