MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

TIRKASHI: EFCC TA BANKADO BADAKALAR DAN TSOHON MINISTA DAYA SAYI GIDAJEN BILIYAN 1 A ABUJA-Karanta Kaji

EFCC: Ta Gano Badakalar Biliyan 1 Da Dan Tsohon Minista Ya Sayi Gidaje Dasu  A Abuja.

Bincike ta nuna yadda dan tsohon ministan birnin Abuja, Shamsudeen ya mallaki gidajen naira biliyan 1 a Abuja

Gwamnatin tarayya na zargin dan ministan da aikata laifi har guda 5
Binciken ta nuna cewa, Shamsudeen ya yi amfani da sunayen wasu kanfanoni waje sayan ƙaddarori ma su yawa Wani mai shaida kuma ma’aikaci a hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Ishaya Daudu ya yi bayani ta yadda ɗan tsohon ministan birnin tarayya ta Abuja, sanata Bala Mohammaed, Shamsudeen ya mallaki gidaje a sassa daban-daban na babban birnin tarayya ta Abuja.
Gwamnatin tarayyar Najeriya na zargin Shamsudeen da aikata laifi har guda 5 a gaban mai shari’a, Nnmadi Dimgba ta babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja. Babbar kotun ta fara sauraran wannan karar ne tun ranar 30 ga watan Mayu na wannan shekara.
Tun farko dai, ana tuhumarsa da aikata laifi 15, amma lauyan gwamnatin tarayya ya sanar da cewa sun yi gyare-gyare domin haɗa kuɗaɗe na gida da na ƙasashen waje da aka samu a cikin asusun ajiyarsa na Standard Chartered Bank.
Dan tsohon ministan Abuja, Shamsudeen Bala Mohammaed Gwamnati ta gurfanar da wanda ake zargi tare da wasu kamfanoninsa guda 4; sun hada da Bird Trust Agro Allied Ltd da Intertrans Global Logistics Ltd da Diakin Telecommunications Ltd da kuma Bal-Ɓ ac Mining Nigeria Ltd, yayin da ake tuhumar su da sace naira biliyan 1.1 dukiyar al’umma.
Majiyar Dandalin Mujallarmu ta tabbatar da cewar, a zaman babbar kotun a ranar Alhamis da ta gabata, lauyan mai gabatar da ƙara Ben Ikanni, ya jagoranci Ishaya Daudu zuwa kotu domin bada shaida.
Daudu ya bayyana cewa, ya san wanda a ke tuhuma ne a lokacin da yake wani binciken akan tsohon ministan Abuja, watau sanata Bala Mohammed inda suka gano wasu chanje-chanje a ƙaddarorin wanda a ke tuhuma. Binciken da aka gudanar ta nuna cewa, Shamsudeen ya yi amfani da sunayen wasu kamfanoni wajen sayan dukiyoyi da dama, kamfanonin sun haɗa da Inter-trans Logistics Global Nig. Ltd. da Balɓ ac Mining Nig. Ltd. da kuma Diakin Telecommunications Ltd. wanda duk suna cikin waɗanda ake tuhuma, an kuma gano cewa wadannan kamfanonin mallakar dan tsohon ministan ne.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-12 — 7:52 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme