MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SO KO KUDI:WANI SAURAYI MAI SHEKARA 27 DAN KABILAR IBO YA AURE BATURIYA ‘YAR SHEKARA 72-(Hotuna)

Wata Gyatuma Yar Kasar Ingila Ta Aure Sa’an Jikanta Na 6 Dan Kabilar Igbo.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Wata gyatuma yar kasar Ingila ta kamu da soyayyar wani matashin dan kabilar Ibo wanda yayi mata magana a shafin sadarwa na Facebook, inda daga nan suka fara soyewa har lamarin ya kai ga aure. Wannan mata mai suna Angela mai shekaru 72 tana da yaya da jikoki shidda, wanda karamin jikanta ma ya girmi saurayin nata da shekaru 6.

Shi kuwa gogan nata wanda ta bayyana sunansa a matsayin CJ, matashine dan kabilar Ibo mai shekaru 27, wanda ya kammala digirinsa na farko.

Sai dai Angela ta koka kan yadda jami’n ofishin jakadancin kasar Birtaniya suka hana sahibin nata izinin shiga kasar UK, duk da cewa tuni an daura musu aure a nan Najeriya, inda aka yi bikin a garin Owerri na jihar Imo.

Ranar aurensu Wani abin mamaki shine Angela ta tabbatar CJ ba kudinta yake nema ba kamar yadda ake samun wasu samarin suna auren tsofaffi domin kudinsu, musamman bayan ta fada masa ita fa tsohuwar direban tasi ce, kuma tayi ritaya, amma gogan nata yace ya ji, ya gani. Ma’auratan Da take bada labara ga majiyar Dandalin Mujallarmu.com, Angela tace “Bayan mutuwar aure na da wata 6, sai ga wani matashi kyakkyawa ya min magana a facebook, daga nan muka fara hira har muka saba, matsalata kadai shine na bashi tazarar shekaru 45, kuma a Najeriya yake zama.” CJ da Angela Angela tace ta samu goyon bayan kananta su duka, a cikinsu akwai mai shekaru 50, 47 da kuma 43, kuma tace sun yi maraba da auren nata, sai dai basu biyo ta Najeriya ba don halartar bikin aurenta da CJ sakamakon a dan kankanin lokaci aka fada musu. CJ da Angela

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-08-26 — 10:43 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme