MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

ZABEN FIDDA GWANI NA JAM’IYYAR APC A KADUNA YA GAMU DA CIKAS

Zaben Fidda Gwani Na Kansiloli Da Jam’iyyar APC Ta Gudanar Yau A Kaduna Ya Gamu Da Cikas Da rashin Tsari

Daga Auwal M Kura

Zaben Fidda Gwani Na Kansiloli Da Jam’iyyar APC Ta Gudanar Yau 29/03/2018 Ya Gamu Cikas Da Rashin Tsari,

Inda Wasu Mazu Dake Birni Da Kyaukan Jahar Basu Gudanar Da Zaben Ba , Kamar Yadda Ya Faru

Ciki Daga Cikin Mazabun Sun Hada unguwar Sunusi Dake Karamar Hukumar Kaduna Da Kuma Rigasa Dake Karamar Hukumar Igabi Da Sauran Wasu Mazabu Da Dama Basu Gudanar Da Zaben Ba, Inda Jama’a Dake Dauke da Katin Shedar Yayan Jam’iyyar APC Ne Suka Fito Tun Safe Amma Har Yamma Babu Wani Wakili Ko Jami’an Zabe Daga Uwar Jam’iyyar APC Ta Jahar Kaduna Da Suka Gani ,Wanda Hakan Ba Karamin Fusata Ya’yan Jam’iyyar Yayi, Inda Wasu Ke Zargin Wasu Shugaban nin Jam’iyyar A Jahar Kaduna Da Kokari Kakabawa Al’umma Wadanda NASA So Da Karfin Tsiya Ta Hanyar Dauki Dora

A Daya Bangaren Kuma Jama’a Da Dama Na Alakatan Hakan Da Rashin Tsari Da Jam’iyyar Bata Dashi Hakan Matsayin Abun Kunya Ne Ga Jam’iyyar APC A Jahar Dama Kasa Baki Daya

Updated: 2018-03-29 — 7:15 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme