MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SIYASA: MATA KU BAWA MIJINA GUDUNMUWARKU YAYI TAZARCE A ZABEN 2019-Inji Aisha Buhari

Mata Ku Taimakawa Mijina Ya Lashe Zaben 2019 Cewar Uwar Gidan Shugaba Buhari-Aisha

Aisha, uwargidan shugaban kasa, a ranar Talata, 4 ga watan Disamba ta bukaci yan Najeriya da su taimaka su tabbatar sun dawo da Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mulki a zaben 2019. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Aisha ta roki matan a lokacin da ta halarci taron shugabannin mata na kasa wanda wata kungiyar siyasa ta shirya domin Buhari da Osinbajo a cibiyar ci gaban mata da ke, Abuja.

Rahoton ya bayyana cewa daraktan labaran Aisha, Suleiman Haruna, yace uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa a zaben da ya gabata mata ne suka jajirce wajen zabar APC. Ta bayyana cewa hakan ne dalilin da yasa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samar da wani shiri don tallafawa mata da yaransu domin a rage yawan talauci a tsakaninsu.

Da ta nemi ayi shiru na minti guda domin karrama sojojin da suka rasa rayukansu wajen tsaron kasar, Aisha ta bukaci gwamnati da ta saki hakkokinsu.

 

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-12-05 — 11:08 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme