MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SIRRIN DA YA SA NA AURI MATA BIYU A LOKACI GUDA- ANGO

Matashin Angon Bashir Muhammad, Ƴya angwance da kyawawan matansa guda biyu masu suna; Nimo da Iqra. An ɗaura auren ne tun a 22ga watan Yunin nan, a kauyen Sinai.

Amina Yusuf Ali

A yayin hirarsa da ‘yan jaridu, Bashir ya bayyana cewa: ya shafe tsawon watanni takwas yana soyayya tare da lallamin waɗannan matan nasa kafin ya kai ga aurensu. Sannan yakan gayyace su gidansa don su saba da junansu.

sirrin da yasa na auri mata biyu

Angon ɗan asalin kasar Somaliya ya bayyana wa majiyarmu dalilinsa na auren mata guda biyu a lokaci guda. Duk da dai a cewarsa auren mace fiye da ɗaya bai saɓa wa al’adarsu ta kasar Somaliya ba, amma auren mace biyu a lokaci guda sabon abu na a wajensu. Ya ce ya yi hakan ne don ya samu zuriyya mai yawa kuma don ya rage wa matan nasa zafin kishi saboda kowacce da ma ya san ba ita kaɗai ce ba, tun kafin ya shigo.

SIRRIN DA NAMIJI: HANYOYIN SAKA MAI GIDA FARINCIKI – UMMULKHAIR

Kuma ya sha tara su ya jaddada musu cewa; yana son kowaccensu ɗari bisa ɗari. Kuma su ma sun gamsu da hakan, shi ya sa ma suka amince suka aure shi. Daga karshe angon ya yi kira ga sauran maza da su yi koyi da shi. Domin abu ne mai ɗaɗin gaske.

https://instagram.com/mujallarmu

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-06-28 — 12:02 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme