MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

SHARHIN KAN TALAUCI DA AKAYI A DUNIYA. kukaran ta

Yaƙi da talauci batu ne da ke ci wa kasashe da dama tuwo a ƙwarya. Wannan shi ya sa da dama daga ƙungiyoyi da cibiyoyin da ke aiki kan raya ƙasa suka mai da hankali wajen yin bincike da gano ingantattun hanyoyin da za a yi amfani da su wajen magance fatara da talauci.

Abin tambaya a nan shi ne, me ake nufi da talauci, ta ƙaƙa za a iya fahimtarsa?

A wani sharhi na musamman da cibiyar ilimi, kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya wato (UNESCO) ta wallafa, ta bayyana cewa za a iya fahimtar talauci ne ta fuskoki guda biyu: wato matsanancin talauci, da kuma talauci sese-sese.Shi matsanancin talauci ana fahimtarsa ne gwargwadon yawan kudaden shigar da mutum ke samu, da wadatar wadannan kudade wajen biyan bukatu na yau da kullum. Wadannan bukatu sun hada da ci da sha da matsuguni da sauransu. A takaice, matsanancin talauci shi ne yanayi na matsi da rashin samun ingantanciyyar rayuwa ta yadda dan Adam zai rayu cikin mutunci ba tare da tagayyara ko tozarta ba.

Talauci sese-sese kuwa ana duba shi ne gwargwadon irin kudaden da mutum yake samu idan aka kwatanta da sauran al’umma. Abin da hakan ke nufi shi ne, za a iya samun bambanci tsakanin kasashe bisa yanayinsu da karfin tattalin arzikinsu.

Alal misali, a kasashen Turai mallakar gida, da samun kiwon lafiya, da cin abinci mai kyau, ingancinsa ya kai rayuwar mai tagomashi a wasu yankunan na duniya. Hakazalika idan ka dauki yanayin rayuwa a kasashen Larabawa masu arzikin man fetur, wanda yake matsayin talaka a wasu kasashen zai iya zama mai wadata ne a wasu kasashen.

Daga cikin alkaluman da ake amfani da su wajen gane talauci, shi ne duk mutumin da yake rayuwa da kasa da dalar Amurka biyu, wato kimanin Naira dari bakwai a kudin Nijeriya (bisa canji na kasuwar bayan fage), to wannan mutumin shi ake kira da talaka.

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-05-27 — 1:01 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme