MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

RASHAWA:KOTU TA YANKEWA WANI TSOHON SHUGABAN KARAMAR HUKUMA DAURIN SHEKARA 6 A GIDAN YARI-karanta Kaji

AN YANKEWA WANI TSOHON SHUGABAN KARAMAR HUKUMA DAURIN SHEKARU 6 A GIDAN YARI

Daga Auwal M Kura

9/1/2018

Wata Babbar Kotun Jahar osun A Ranar Litini 8/1/2018 Ta Yankewa Wani Tsohon Shugaban Karamar hukumar Jahar Mai Suna Rufus Wole-ojo Daurin Shekaru Shida A Gidan Yari Bayan Kamashi Da Lafin Handame Naira Milyan 22m.

Hukumar Yaki Da Rashawa Dayiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa ta (EFCC) Ce Ta Gurfanar Da Mai Lefin Tun Ranar Ashirin Da Takwas Ga Watan Mayu Shekarar Dubu Biyu Da Sha uku Bisa Laifuka Guda Uku, Da Suka Hada Da Zamba Cikin Aminci ,Yin Amfani Da Matsayin Domin Biyan Bukata Ta Kashin Kansa,Bawa Sata Kariya.

Daya Daga Cikin Laifukan Da Aka kama Mai lefin Akwai Amfani Wani Kamfanin Nasa Na Kasuwanci A Shekarar Dubu Biyu Da Shida Wajan Karkatar Da Sama Milyana Ashirin Da Dubu Hamsin Da Takwas Da Naira Ashirin Da Daya Da kobo Talatin N22,058,021.30k Na Karamar Hukumar Orolu Local A Shekarar Dubu Biyu Da Shida
Yin Wadaka Da Dukiyar Karamar Hukumar tare Da Bannatar Gami Da Banzantar Da Amanar Da Akabashi Lokacin Yana Shugabantar Karamar Hukumar ta Orolu

A Karshe Dai Mai Shari’a David Oladimeji Ya Yanke Masa Hukuncin Shekara Shida Bisa Kamashi da Yayi Da Laifuka Biyu Inda Ko Wani Laifi Zaiyi Tsawon Shekaru uku

Sai Da Daga Baya An Sake Karanta Shari’ar Inda Mai Shari’a Dimeji Ya Sami Mai Lefin Da Laifi Guda Daya
Wanda Hakan Zaisa A Rage Daurin Zuwa Shekara Uku

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2018-01-09 — 4:21 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme