MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Ranar Demokaradiya: Karanta kaji sakon Yan Najeriya zuwa ga Shugaba Buhari

Ranar 29 ta watan Mayun Shekarar 1999 Najeriya ta koma mulkin dimokradiya daga mulkin soja kuma tun daga lokacin aka ayyana ranar a matsayin ranar Dimokradiya wadda kowace shekara ake tunawa da zagayowarta kamar yadda ake yi yau a duk fadin kasar.

A wani gefen kuma gwamnatin APC a karkashin shugabancin Muhammad Buhari ta cika shekaru uku cur tana mulkin kasar. Gwamnatin tasa tana samun yabo daga wasu ‘yan Najeriya dake ganin ta taka rawar gani, musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa da fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram dake tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Amma ‘yan babbar jam’iyyar adawa ta PDP suna ganin babu wani abun a zo a gani da gwamnatin APC din ta tsinana cikin shekaru ukun da tayi tana mulki.

To saidai gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce su aikin raya kasa suka sa agaba ba maganar jam’iyyar PDP ba.

Gwamnan na jahar Nija yace ba maganar wata jam’iyya ko ma PDP, jam’iyyar da ya ce ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16.

Ya ce shi kansa ya yi PDP din. Sun san irin dukiyar da aka samu a can baya da irin almubazarancin da aka yi. Gwamnan ya ce da gwamnatin shugaba Buhari bata zo ba da watakila ma yanzu babu kasar saboda irin mawuyacin halin da kasar zata shiga.

Duk da furucin gwamnan, jam’iyyar ta PDP ta ce tana ganin haske a gaba dangane da babban zaben badi kamar yadda shugaban jam’iyyar na jihar Neja Barrister Tanko Beji ya fada. Y ace sun yi na’am da irin goyon bayan da jama’a ke basu. Yanzu dai ana jiran lokaci ne kawai.

ranar 29 Watan Mayu ne ake bukuwan ranar zagayowar komawa ga mulkin Dimokradiya a kasar.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-05-29 — 4:05 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme