A ranar alhamis data gabata ministan harkokin kudi ta Najeriya Mr Kemi Adeosun ta shirya wani gagarumin taro a jihar Enugu.

Wannan taro an gudanar dashi ne don wayar da kan al’ummar Jihar Enugu game da yadda biyan haraji keda matukar amfani da kuma bada gudunmuwa a jiha.

Taron ya samu halartar manyan baki daga cikin garin na Enugu da suka Hada da maigirma gwamann Ifeanyi Ugwuanyi da kuma akawu janar na jihar Enugu Alhaji Ahmed Idris, tare da Shugaban majalisar wakilai na jihar Enugu Mr Edward Ubosi.

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu, keda labari daga wajen taron inda ministan kudi Kemi Adeosun ke jawabi, tace kungiyar VAIDS kungiya ce da aka kirkiro ta don kawo cigaba ta hanyar karbar haraji a jihar Enugu da Nijeriya baki daya tare da fadada hanyoyin samun kudin shiga a Najeriya.

Adeosun ta bayyana damuwarta cewa akan cewa haraji da kuma GDP babban hanya ce ta magance talauci da koma Baya ga tattalin arzikin kasa,,inda tace cewa yanzu a kasashen duniya Najeriya itace kasa mafi kaskancin samun kudin shiga a bangaren haraji kashi 6%100, a maimakon mutane sama da Miliyan 70 ace sune ke biyan haraji a Najeriya amma kwata kwata mutane Miliyan 14 kadai ke biyan  haraji. Adeosun ta Kara da cewa yazama wajibi ga kowane dan Najeriya ya rinka biyan haraji akan lokaci, kan yadda gwamnati ta tsara.

Har ila yau Kemi Adeosun ta cigaba da cewa Idan har muna son samun cigaba da wadatar kasa mai dorewa yanzu da nan gaba, to yazama dole mu tashi mu gina kan mu da kan mu ta hanyar biyan haraji a bisa ka’ida.

Adeosun tace har kullum ‘yan Najeriya suna dogara ne kawai akan man fetur saboda suna ganin cewa itace kadai hanya da Najeriya ke iya samun kudin shiga.

Da ace akai akai ‘yan Najeriya suna biyan haraji to da tuni Najeriya ta Wuce inda ake tunani a bangaren tattalin arzikin kasa, sakamakon koma baya, Inji ministan.

Bugu da kari ministan tayi gargadin cewa ba’ a kangewa kowa biyan haraji ba matukar dan Najeriya ne kuma yakai mizani na lokacin daya kamata ace ya fara biya, saboda haka yazama wajibi a garemu mu rungumi wannan sabuwar hanya ta karbar Haraji maisuna VAIDS don inganta raguwar mu yanzu da nan gaba_Cewar ta.

Akarshe gwamnan jihar Enugu Ifeanyi ya bayyana godiyar sa ta musamman ga ministan ta kudi Kemi Adeosun bisa namijin kokarin datayi wajen kawo sauyi acikin jihar Enugu, ta hanyar bullo da sabuwar kungiya maisuna VAIDS mai kula da sashen haraji na jihohi da kasa baki daya.

Gwamnan ya kara da cewa haraji hanya ce ta cigaba ga kowace jiha idan ta maida hankalinta  akai da kuma ita kanta gwamnatin tarayya, inda acikin bayanin gwamnan yake jawabin cewa hanyoyi da dama da suka lalace a jihar ta Enugu anyi gyaran sune acikin kudaden Harajin da ake amsa hannun al’umma inda kuma aka sayi magunguna da kuma gyaran asibitoci dake bukatar gyara na musamman a jihar, tare da bunkusa ilimin zamani.

Har ila yau gwamna Ifeanyi ya mika godiyar sa ga mutanen jihar Enugu bisa namijin kokari da sukayi wajen jajircewa suna biyan haraji bisa ka’ida akan lokaci, inda karshe ya shawarce su da kada suyi kasa a gwaiwa ko nuna gajiya akan haka saboda sune ke da ribar abin ba gwamnati ba.

This website uses cookies.