MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Oloyede ya soki batun neman rage kudin jarabawar JAMB

Shugaban Hukumar Shirya

Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB, Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa ya zuwa ranar 29 Ga Augusta, dalibai 24,148 ne suka samu nasarar shiga manyan makarantun kasar nan.

Daga nan kuma sai ya yi watsi da
kiraye-kirayen da wasu ke yi, su na
korafin a rage kudin jarabawa, a
bisa dalilin su cewa sun yi yawa
matuka.

Shugaban na JAMB ya ce masu yin
wannan korfin ba su ma da wata
hujja ko dalilin korafin, kuma ba za
a ce kudin ma sun yi yawa ba.
Kimanin dalibai miliyan 1,662,762
suka rubuta jarabawar UTME ta
neman shiga jami’a tsakanin watan
maris, 9 zuwa 19 na cikin watan.

Kakakin Hukumar, Fabian Benjamin
ne ya bada karin hasken yawan
daliban da aka dauka zuwa manyan
makarantu a cikin wata hira ta
wayar tarho da ya yi da PREMIUM
TIMES.

Har ila yau, Oloyede ya ce ai kudin
jarabawar JAMB a Najeriya ya ma fi
na kowace kasa a duniya arha.

Ya ce JAMB ta na saida fam din a
kan naira 5,000, amma har naira
bilyan 7.8 ta aika wa Gwamnatin
Tarayya a matsayin kudaden shiga.
“Shin me ya sa ba za su nemi WAEC
ko NECO su rage na su yawan kudin
jarabawar ba? Me ya sa kuma bas u
nemi NABTEB ta rage na ya kudaden
jarabawar ta ba?

“Kawai don a yanzu an ga mu na
ririta kudaden da muke samu ne,
kuma su na isar hukumar gudanar
da ayyukan ta, har ma a samu rarar
kudade masu yawa. Shi ne a yanzu
wasu ke cewa wai mu fito mu rage
kudaden.” Inji Oloyede.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-31 — 8:53 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme