MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

NOMA TUSHEN ARZIKI: GWAMNATIN NAJERIYA TA SAMU NAIRA BILIYAN 212.73 A FANNIN NOMA A MULKIN BUHARI-Karanta Kaji

Najeriya Tasamu Zunzurutun Kudi Kimanin Naira Biliyan 212.73 A Bangaren Noma A Karkashin Buhari

Najeriya ta samu naira biliyan 212.73 daga fitar da albarkatun noma kasashen waje a karshen kwata na hudu a 2016, an bayyana haka ne a wani littafi mai suna: “Making steady, sustainable progress for Nigeria’s peace and prosperity: a mid-term scorecard on the President Muhammadu Buhari administration,” tawagar sadarwa na shugaban kasa ne suka wallfa littafin.
Za’a gabatar da littafin ne a taron da za’a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba a Abuja, kamfanin dillancin labarai (NAN) ce ta gano hakan.
Ta kara da cewa ma’aikatar zata dauki matakinta na farko a hanyoyin kiyaye albarkatun kasar Najeriya da ake turawa kasashen waje daga rashin amincewa ga kasuwannin waje.
Masu magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, Garba shehu da Laolu Akande ne suka tantance littafin.
Littafin ya kasance dauke da sanannen nasarorin gwamnatin APC da Muhammadu Buhari ke shugabanta tun daga lokacin da aka kafa ta a ranar 29 ga watan Mayu, 2015.
Shugaba Buhari ya rubuta shafi dake dauke da gabatarwar littafin mai dauke da shafi 348, mai dauke da nasarorin ma’aiktun tarayya da wassu bangarori cikin shekaru biyu da suka gabata Kungiyar masu watsa labarai na shugaba Buhari ta kara da taimako ga tarin arziki a bubuce da na bayyane.
Ana sa ran Prince Tony Momoh ne zai bayyana littafin sannan babban jigon jam’iyyar APC Bola Tinubu ne zai gabatar da jawabai kan littafin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-13 — 12:25 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme