MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MIJINA YA DAINA SADUWA DANI – INJI WATA MATA

Mijina Ya Daina Saduwa Dani – Inji Wata Mata Mai Juna Biyu Data Nemi Kotu Ta Raba Aurensu

Daga Auwal M Kura
15 /04/2019

Wata Mata Mai Dauke Da Juna Biyu Mai Suna Lauratu Abdullahi, Yar Kimanin Shekaru 30, Ta Nemi Kotun Shari’ar Musulunci Dake Magajin Gari A Jahar Kaduna Ta Raba Aurenta Da Mijinta, Saboda Rashin Saduwa Da Mijin Baiyi Da Ita.

Kamar Yadda Lauratu Ta Shaidawa Koto Cewa Mijinta Yahya Tanko, Bashi Da Aiki Daya Wuce Cimata Zarafi,Rashin Biya Mata Hakkokin Da Suka Wajabba A Kanshi matsayinta Na Matarshi,

Lauratu Mai Kimanin Ya’ya’ Biyar Ta Kara Da cewa Tsawon Wata Hudu Ke Nan Mijin Nata Baya Kwanciya Da Ita (Saduwa) Sai Dukanta Da Yakeyi kana Kuma Bai Damu Da Wani Hali Take Ciki Ba,Har Abinci Ya Daina Bata Tsawon Wannan Lokaci, Shiyasa Nake so Ya Sakeni.

A Nashi Bangaren Mijin Matar Yahaya Tanko , Ya Musanta Wannan Zargi Da Matarshi Take Tuhumarsa Dashi A Gaban Kotu,Inda Ya Shadawa Kotu Cewa Shi Har Yanzu Yana Matukar Kaunar Matarsa.

Yahaya Tanko, Ya Kara Dacewa” Babu Yadda Za’a Matar Da Ba’a Saduwa Da’ita Ta Dauki Ciki,Kuma Ni Matata Yanzu Haka Tana Dauke Da Cikin Wata Hudu,Don Haka Ba Gaskiya Bane Cewa Bana Saduwa Da Ita” cewar Mijin.

A nashi Bangaren Mai Shari’a Malam Musa Sa’ad, Ya Tambayi Mai Kara Lauratu Abdullahi,Kan cewa Dagaske Ne Maganar Mijinta,Tana Dauke Da Juna Biyu, Inda Ta Amsa Da Cewa “Eh” Amma Ta Samu Cikin Ne Tun Watan Farko Natsawon Watanni Hudu Da Maigidan Nata Ya kauracewa Saduwa Da Ita.

Bayan Sauraron Ko Wani Bangare Mai Shari’a Malam Musa Sa’ad Ya Dage Karar Inda Ya Nemi Kowani Bangare Ya Gabatarwa Da Kotu Da Kwararan Shedu Kafin Zaman Kotun Na Gaba

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-04-16 — 10:07 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme