MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MATA GARE KU: ABUBUWA 10 DA ZASU SA KI ZAMA TAURARUWA WAJEN IYA DAFA ABINCI.

Dabaru Guda 12 Da Za Su Mayar Da Ke Tauraruwa A Kicin

Wannan ci gaba ne na dabarun girkin da na wallafa a baya wanda zaku iya samu a nan:

Wadannan dabarun da na tattaro za su taimaka maki matuka wajen kara ingancin harkokin ki na kicin su kuma kara maki kwarewa wajen warware matsalolin da za su iya taso maki.

Akasi a dahuwar abinci

1. Idan kika yi kuskure gishiri yayi yawa a abincin ki ko a miyar ki, abinda za ki yi shine, ki fere dankali ki jefa a ciki, dankali zai shanye gishirin.

2. A lokacin da abincin ki ya kone yake kauri, ki samu bredi mai yanka yanka guda daya ki dora a kan abincin, bredin zai nade kaurin. Amma fa ki yi hankali kar ki kankaro wajen da ya kone yayin da kike diban abincin.

3. Idan kuma miyar tumatir kike yi ta kone, zaki sauke ki sauya tukunyar sannan ki na kara sikari kadan kadan har sai dandanon kauri ya kau.

4. Idan mai ne ya yi yawa a cikin miya, zaki jefa kankara karama, zaki ga ta  janyo man guri daya, sai kawai ki kwashe.

Ajiye Ajiye a Kicin

5. Idan ba kya san dankallin da kika ajiye a cikin buhu ya fara tsiro, saka tuffa guda daya a ciki

6. Wani lokacin zaki ajiye rufaffun robobi da zummar zaki zuba wani abu a cikin su nan gaba, amma idan lokacin amfanin yayi sai ki ji suna wari, zaki iya tabbatar da hakan bata faru ba ta hanyar zuba gishiri kadan a ciki kafin ki yi ajiyar.

7. Kar ki Ajiye ayaba guri daya da sauran kayan itace domin tana sakin wata iska mai saka su nuna da wuri wanda zai iya haifar da saurin lalacewa

8. Idan gishirin ki ya fara curewa saboda damshi, ki jefa kwayoyin shinkafa a ciki, za su shanye damshin.

9. Idan kika hada kofunan gilasai biyu kika kasa rabasu, ki saka kankara a cikin na saman, na kasan kuma ki saka shi a cikin ruwan dumi, na kasan zai fadada, na saman ya tsuke wanda zai saukaka raba su

10. Karki taba yin ajiyar lemo, lemon tsami da tumatir a cikin firji saboda sanyin yana rage musu kanshi da dandanon su

Tukunya

11. Idan tukunyar aluminium kike amfani da ita kuma ta fara kodewa, na san kin san yadda zaki wanke bayan yayi ta sheki, toh amma cikin fa? Abun da zaki yi shine ki zuba bawon tufa a ciki da ruwa ki dafa, zai rage mata kodewar.

Man suya

12. Idan kina son ki kara amfani da man da kikayi suya da shi kuma ba kya son kamshin abunda kika soya ya fito, ki soya danyar citta kadan a ciki, zai kawar da kamshin.

Cinnaku

13. Idan cinnaku sun addabe ki a kicin, ki nemi hudar da suke fitowa ki shafa vaselin a gurin, ba zasu iya tsallakewa ba. Idan kuma ta karkashin kofa suke shigowa, to ki ja layi da alli a gurin, shi ma ba za su ketare ba.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2017-09-05 — 6:26 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme