MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Masoya Buhari sun yi tir da kalaman Trump

Sanarwar ta kara da cewa Shugaban Amurkan ya saba yin kalaman batanci kan wasu shugabannin kasashen duniya.

“Mun san ba sabon abu ba ne cewa Shugaba Trump na yi wa shugabannin duniya rashin mutunci; kalamansa kan firai ministan Canada Justin Trudeau, inda ya bayyana shi da ‘mai sanyi-sanyi’.”

“Ya taba bayyana wani mataki da Shugabar Jamus, Angela Merkel ta dauka a matsayin na ‘rashin hankali’, ko kuma sakon Twitter da ya yi kan Theresa May ta Birtaniya, da kuma kalaman da aka ce ya yi bayan ya gana da Shugaba Buhari.”

Jaridar Financial Times ta Burtaniya ce tabwallafa labarin da ke cewa Shugaba Trump ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mutum mara kuzari.

Sai dai fadar shugaban Najeriya ta ce ba za ta ce uffan ba kan kalaman da aka ambato shugaban Amurka Donald Trump ya yi a kansa.

Kakakin shugaban kasar, Mr Femi Adesina, ya gaya wa BBC cewa ba za su ce uffan a kan batun ba saboda ba shi da tushe bare makama.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme