MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MASHA ALLAH: RUNDUNAR SOJOJI SUN KWATO DUKA GARURUWAN DA ‘YAN BOKO HARAM SUKA MAMAYE A BORNO

Rundunar Soji sun kwato duka garuruwan da Boko Haram suka mamaye.

Kwanel Onyewa Nwachuku ya ce sun fatattaki ‘yan Boko Haram din daga Sambisa da Alagarmo. Babu wani wuri da ke hannun ‘yan kungiyar a halin yanzun.
Ya kuma ce a ‘yan kwanakin nan an samu kwato kauyaku guda 630 da kuma samun kashe ‘yan kungiyar guda 82. – Onyewa ya ce ana kira ga mutane da su dawo mazaunan su don cigaba da gudanar da harkokin su.
A ranar Juma’a ne Rundunar Soji ta ce ta kwato dukkan wuraren da ‘yan boko haram suka mamaye a baya. Kwanel Onyewa Nwachuku wanda shine ya fadi hakan a wata jawabi da ya gabatar a Maiduguri.
Onyewa shine mataimakin Darakta mai gudanar da mu’amala tsakanin sojin da farar hula.
Onyewa ya ce rundunar Soji a karkashin salon aiki mai taken Lafiya Dole ta samu nasarar fatattakar ‘yan Boko Haram daga manyan hedkwatocin su na Sambisa da Alagarmo,rundunar Sojin kuma ta ci gaba da gudanar da harkan tsaro a yankunan.
Onyewa ya yi kira da a yi watsi da labaran karya na cewa wai har yanzun akwai kananan hukumoni guda 27 da suke hannun ‘yan Boko Haram.
Ya ce watsa irin wannan karya ba komai bane illa yunkurin boye asalin halin tsaro da Arewa maso Gabas ke ciki.
Ya kara da cewa an gudanar da wasu salon ayyukan Sojan masu taken DEEP PUNCH, CHIKIN GUDU da RAWAR KADA.
An gudanar da su ne tare da hadin gwiwan Rundunar Gamayyar Sojin kasashe wato Multinational Joint Task Force (MNJTF).
Onyewa ya ce Boko Haram bata rike da wani yanki, hasali ma bata da karfin yin hakan. Bugu da kari Soji na bin sahun ma wadanda aka fatattakar ne. Ya ce a ‘yan kwanakin nan an kashe ‘yan Boko Haram kimanin 82 an kuma kwato kauyaku kimanin 630.
Don haka ana ba wa mutane karfin gwiwan su dawo mazaunan su don cigaba da gudanar da harkokin su.

(Visited 5 times, 1 visits today)
Updated: 2017-09-25 — 10:51 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme