KARANTA KAJI: MANYAN DALILAI 6 DAKE HAIFAR WA MATA HAIHUWAR JARIRAI ‘BAKWAIN’I

          Manyan dalilai guda 6 da ka iya sanya mace haifan jarirai ‘Bakwaini’

Wani shahararren masanin aikin likitanci mai kula da kiwon lafiyan mata Dakta Chris Abumchi ya bayyana Najeriya a matsayin kasar ta uku cikin kasashen da aka fi haihuwar Bakwaini

Jaridar Premium Times ta ruwaito likitan yana fadin cewa a duk haihuwa 10, ana samun jariri bakwaini guda 1.
Dandalin Mujallarmu,ta ruwaito likitana ya yi bayanin haihuwa bakwaini a matsayin yadda ake haihuwar jariri ba tare da wasu sashin jikinsa sun kammala haduwa ba, sakamakon haihuwarsa kafin watanni 9.
Dakta Chris yace dalilan dake sa ake haihuwa Bakwaini sun hada da:
1. Shan taba sigari
2. Mace mai ciwon siga
3- Amfani da magunguna ba tare da izinin likita ba
4- Mace mai shan giya
5- Zama da yunwa
6- Rashin samun kwanciyar hankali Da wannan ake yin kira ga mata da masu dauke da juna biyu da su dinga zuwa Asibiti da zarar sun fara zubar da jini ko jin ciwon jiki.

This website uses cookies.