MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

MADALLA: YANZU NAJERIYA TANA DA ISASSHEN ABINCIN DA ZAI IYA MAGANCE KARANCIN ABINCI A SHEKARAR 2018-Inji Minista Noma

Najeriya na da isashen abinci don magance karancin abinci a 2018 – Minista

Jiya Lahadi gwamnatin tarayya ta bada sanarwa akan yadda Najeriya tasamu wadatar abinci yanzu,wanda ganin haka yasa ake tunanin yanzu Najeriya tana da isasshen abincin da zai iya magance duk wata matsala da ka iya zuwa da dawo na karancin abincin a wasu jihohi a shekarar 2018.

Ministan Noma da cigaban karkara, Audu Ogbe ne ya bayyana haka a jihar Katsina.

Ministan yayi magana a taron hadin kan sasashe don samar da kudi ga cigaban harkar noma (IFAD)/manufar dubawar canjin yanayi na Gwamnatin Tarayya karo na biyu, taron magoya bayan kasuwancin noma. Mista Ogbeh ya samu wakilcin babban mai bada shawara Auta Appeh a taron. Najeriya na da isashen abinci don magance karancin abinci a 2018 – Minista
Najeriya na da isashen abinci don magance karancin abinci a 2018 – Minista “Wassu jihohi a yankin Arewa-maso-gabas da sauran yankunan kasan suna iya fuskantar karanci a kayan gona a 2018 saboda canjin yanayi da al’amuran yanayi.
“Duk da haka, yunwa baya daga cikin zancen, ina iya tabbatar muku cewa mun ajiye musu isasshen kayan abinci ta shirinmu tsaro kan kayan abinci,” a cewar shi. Ministan ya shawarci manoma da su daina ka da itatuwa saboda adanan yanayi.
Mista Ogbeh ya fada cewa yanke itatuwa ya kan bude kasa ga kwararowar Hamada, yashewar kasa da sauran abubuwa dake iya canja yanayi wanda hakan yana shafar yanayi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-13 — 11:59 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme