MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

LABARIN WANI BAWAN ALLAH DA YAKE DAB DA RASUWA

Wani Bawan ALLAH Da Yake Kan Gargarar Rasuwa, Sai Dangi Suka Kewaye Shi SunaTa Kuka.

.
Sai Ya Ce:”Ku Tashe Ni Zaune”
.
Sai Suka Zaunar Da Shi Sai Ya Fuskance Su Ya Dubi Mahaifinsa Ya Ce:”Baba! Me Yasa Kake Kukan Rabuwa Da Ni???”
.
Ya Ce:”Ina Jimamin Rashinka Da Yadda Zanyi Da Kewarka Bayan Ka Rasu!”
.
Sai Ya Juya Ga Mahaifiyarsa Ya Ce:”Umma! Me Yasa Kike Kukan Rasa Ni???”
Ta Ce:”Saboda Zan Shiga Quncin Rayuwar Rasaka!”

.
Sai Ya Juya Ga Matarsa Kefa Me Yasa Ki Kuka???
.
Sai Ta Ce:”Zan Rasa Dadin Zaman Da Muka Yi Gashi Kuma Ban San Hannun Wanda Zan Fada Ba”.
.
Sai Ya Juya Ga ‘Yayansa Kufa Me Yasa Ku Kuka???rasuwa .
Suka Ce:”Saboda Zamu Zama Marayu Bamu San Irin Wahalar Da Zamu Shigaba Bayan Baka Nan”
.
Don Allah Idan ku Karanta ku dinga yin Like & Comment ko kuma kuyi Share domin ‘yan uwan Mu su Amfana.
.
Daga Nan Sai Ya Dube Su Ya Fashe Da Matsanancin Kuka Gaba Daya Suka Dube Shi Kai Kuma Me Yasa Ka Kuka???
.
Ya Ce:”Naga Kowa Yana Kukan Rasa Ni Ne Saboda Bukatar Qashin Kansa.
.
Shin a Cikinku Akwai Wanda Yake Kuka Saboda Doguwar Tafiyar Dake Gabana???
.
Koko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda Rashin Isashshen Guzuri Na???
.
Ko Akwai Wanda Yayi Kuka Don Za’a Turbudani a Turbaya???
.
Ko Abin Da Zan Tarar Na Mummunan Hisabi???
.
Ko Ko Akwai Wanda Yake Kuka Saboda Tsayuwata a Gaban Rabbil Izzati Bansan Me Zan Tarar Ba???
.
Daga Nan Sai Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Sai Sukai Kansa Suka Juya Shi Sai Sukaga Ashe Har Rai Yayi Halinsa Ya Rasu!.
.
HAQIQA DUNIYA BATA DA TABBAS!
.
YA ALLAH! KASA MUYI KYAKYKYAWAN QARSHE, YA ALLAH KAYI MANA KARIYA DA RADADIN FITAR RAI, YA ALLAH KAYI MANA GAMDA-KATAR A LOKACIN KARBAN RAYUKANMU YA ZAMA KAMAR NA SALIHAN BAYINKA CIKIN RUWAN SANYI ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA AMEEN

Domin Kallon Sababbin fina finan Hausa Cikin sauka sai kuyi downloading App na Mujallarmu Tv a nan:
Download Mujallarmu TV (284 downloads)

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-07-01 — 1:11 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme