MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

LABARI DA DUMI DUMI: WANI SOJA YA BINDIGE KAFTIN DA WASU ABOKAN AIKIN SA 4 DAGA BAYA YA KASHE KANSA-Karanta Kaji

Wani Soja Ya kashe Abokan Aikin Sa 4 Tare Da Kaftin,Daga Baya Shima Ya Kashe Kansa

Wani saja, Silas Ninyo (93NA/36/2608), a hukumar sojin Najeriya ya bindige kaftin T. Mani saboda ya hana shi dukan wasu farar hula a Chibok dake Jihar Borno. Jami’in sojin Najeriya ya bindige kaftin da wasu mutum 4 kafin ya kashe kan sa Margayi kaftin T. Mani
Wani rahoton jami’an soji (mai lamba 64) da jaridar Saharareporters ta samu da yammacin yau ya tabbatar da cewar Kaftin T. Mani mai jagorantar rundunar soji dake aikin samar da tsaro ga masu ibada a garin Chibok ya rasa ran sa bayan da wani Saja Silas Ninyo ya bindige shi saboda ya tsawatar masa yayin da yake dukan wasu farar hula babu dalili.
Hakazalika saja Ninyo ya bindige kan sa bayan bindige karin wasu mutum 4. Lamarin ya faru ne yayin da Kaftin Mani da wasu sojojin su ka yi kokarin kwace bindigar Saja Ninyo bayan hana shi dukan farar hular.
Gawar sojojin na dakin ajiyar gawa dake asibitin sojoji na Yola kamar yadda rahoton ya bayyana.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-12 — 8:23 pm

1 Comment

Add a Comment
  1. Rufa'i Abubakar

    To ALLAH ya, kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme