LABARI DA DUMI DUMI: CUTAR LASSA FEVER TA KASHE KWARARRUN LIKITOCI BIYU A JIHAR EBONY-Karanta Kaji

Labari  Da Duminsa: Cutar  Lassa  Fever Ta Kashe  Kwarrun  Likitoci  Biyu  A Jihar Ebonyi.

marubuci:Haruna  Sp Dansadau.

Rahoton  da muke samu  daga Babban asibitin  jihar Ebonyi a safiyar yau litinin 15 ga watan janairu.

Cutar zazzabin lassa Fever ta kashe  wasu  kwararrun likitoci  biyu dake aiki Asibitin Abalikiti dake jihar ta Ebonyi.

Har ila yau Dandalin Mujallarmu, ta samu karin  bayani  daga  wasu  masu aiki  a asibitin, inda suka shaidawa  manema  labarai sunayen  malaman  asibitin  biyu  da suka  Mutu.

Ga sunayen  kamar  haka.

1- Abel Sunday:- Abel Sunday kwararren likita  ne a bangaren  Ido  da  hanci (Otorhinolayngology)

2- Dr Ali Felix:- Shima kwararren likita  ne  daya  kwarai  fannin magunguna.

Dukkan likitocin  biyu sun mutu  a bakin  aiki  sanadiyyar kamuwa  da  cutar ta lassa Fever  daga wasu  majinyata dake dauke  da ita a asibitin.

Bugu da kari ma’aikatan  aibitin  sun  Nuna rashin jindadin  da shiga damuwa bisa  wannan  babban  rashi da sukayi  na manya  ma’aikata biyu a lokaci daya.

Idan  zaka  bamu  shawara  ku  turo  muna  labari akan abinda dake  faruwa  yankin  ku/ki a tuntube mu akan  Facebook@mujalarmu ko kuma  a WhatsApp  07035169818.

Tunatarwa Kan Cutar Lassa Fever:

Cutar lassa Fever ana gane  mai  dauke  da ita  ne idan  ya kamu  da  ita  tabbbas.

Alamomi  guda  4 ne

1- Mutuwar  Jiki, zaiji  jikinsa ya  mutu sosai.

2- Matsanancin  ciwon kai.

3- Amai

4- Yawan  jin  ciwon  gabobi  akoda  yaushe.

Allah  ya kyauta  ya kuma  muna  tsare  daga  duk  wata  cuta  Ameen.

This website uses cookies.