MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

LABARI CIKIN HOTUNA- Dan takarar Shugabancin Najeriya Usman Ibrahim Alhaji ya Ziyarci Manyan Sarakunan Jihar Kebbi

Dan Takarar Shugaban kasar Najeriya Usman Ibrahim Alhaji a karkashin tutar jam’iyar NRM ya kai zigayar girmamawa ga wasu manyan Sarakuna na Jihar Kebbi.

Ya fara ziyarar ne daga Fadar Mai Martaba Sarkin Kebbi Inda ya Samu goyon bayansa Dari bisa Dari, Sannan ya sa albarka da yi masa addua da fatan nasara, sannan kuma ya Kara da bada shawarwari ga dan Takarar kuma ya bayyana farin cikinsa ganin ya bashi mahimmanci akan ziyara ta musamman da ya kawo masa kafa da kafa had fadarsa. Kamar yadda jaridar Mujallarmu ta rawaito mana

Daga nan kuma dantakarar Ya Ziyarci Mai Martaba Sarki Sarkin Argungu inda shima ya nuna farin cikinsa kan irin yadda ya nuna cewa lallai muna da mahimmanci agare shi har gashi ya zo har gida don ya bayyana mana kudurin sa na Neman Shugabancin Najeriya a karkashin Jam’iyar National Rescue Movement (NRM).

Kuma dantakarar bai gajiya ba inda a karshe ya je Masarautar Kalgo inda yake da sarauta yakai gaisuwa kuma nan ma ya bayyana kudurin sa na neman takarar Shugabancin Najeriya. A nan ma ya samu Goyon bayan Masaurata kuma Sarki ya yi masa addu’o’i da fatar alheri.

Daga karshe a Wata ganawa da Mujallarmu tayi da shi, Usman Ibrahim Alhaji ya bayyana farin ciki yadda Wadan nan masarautu suka karbeshi hannu biyu-biyu. Kuma yayi Kira ga matasa da su shigo Jam’iyar NRM domin an bude jam’iyar ne domin su fito kwansu da kwarkwata don zamu fitowa takara a Jam’iyar ba tareda sun kashe kudi ba.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-28 — 4:06 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme