MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

Ko na fadi zaben fidda gwani ba zan fice daga PDP ba –Inji Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa

wanda dan takarar shugabancin
Najeriya ne a karkashin jam’iyyar
PDP Sule Lamido ya bayyana cewa
ba zai fice daga jam’iyyar ba koda ya
fadi a zaben fidda gwani.

Ya bayyana haka ne a ganawa da ya
yi da manema labarai a garin Jos,
bayan ganawa da ya yi da Jeremiah
Usaini.

Idan ba a manta ba a kwankin
bayan Lamido ya ziyarci jihar Filato
inda ya sanar ya ‘ya’yan jam’iyyar
PDP a jihar muradin sa na yin
takarar shugabancin kasa Najeriya.
Ya ce duk wadanda suka fito takarar
shugabancin Najeriya a jam’iyyar
PDP na da kwarewa kuma yana da
yakinin cewa dukkan su na yi don
kasa ne ba don san kan su ba.

” Wannan shine babban dalilin da ya
sa ko da na fadi zaben fidda dan
takara ba zan fice daga jam’iyyar ba,
saboda akidar mu daya ne dukkan
mu.

Bayan haka Lamido ya karyata rade-
radin da ake ta yadawa cewa wai ya
fito takarar shugabancin Najeriya ne
da daurin gindin tsohon shugaban
kasa Olusegun Obasanjo.

” Ina tabbatar muku da cewa da
zaran na zama shugaban kasa a
Najeriya zan tabbatar da tsaro a ko-
ina a kasar nan sannan zan bunkasa
tattalin

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme