MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KO KUBI MATAKIN TRUMP KO KUMA KU RUFE MANA BAKI — SAKON SAUDIYA GA FALADDINAWA

“Ko Falasdinawa su bi matakin Trump,ko kuma su yi mana shiru”
— Sakon Yariman Makka Muhammad bin Salman Ga Falasdinawa
Jaridun Amurka sun rawaito cewa,yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya,Muhammad bin Salman ya kira Falasdinawa da su bi matakin Trump na maida Qudus helkwatar kasar Yahudu,ko kuma su daina kokawa.
02.05.2018 ~ 02.05.2018
Jaridun Amurka sun rawaito cewa,yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya,Muhammad bin Salman ya kira Falasdinawa da su bi matakin Trump na maida Qudus helkwatar kasar Yahudu,ko kuma su daina kokawa.
Bin Salman ya yi matukar sukar shugabannin kasar Falasdinu,musamman ma Muhammad Abbas,wanda yake tuhuma da kin amfani da damar da ya samu na cim ma zaman lafiya.
A rawaito cewa,yariman ya furta wadannan kalaman yayin wata ganawar sirri da ya yi da shugabannin kasar Yahudu a New York a ranar 27 ga watan Maris.
Kazalika ya kara da cewa,
“A shekaru 10 da suka shude,shugabannin Falasdinu sun yi watsi da duk wata damar samar da zaman lafiya mai dorewa da aka gabatar musu.Shi yasa lokaci ya zo da ya kamata a ce,sun yi na’am da matakan Trump,ko kuma su rufe bakunansu”.
Ranar 6 ga watan Disambar bara,shugaban Amurka,Donald Trump ya yi matukar fusata Falasdinawa,sakamakon matakin dage ofishin jakadancin kasarsa daga Tel Aviv zuwa tsarkakken birnin Qudus,wacce ya ayyana a matsayin sabuwar helkwatar Isra’ila.Wanda hakan ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.
Abinda yasa Falasdinawa, wadanda ke mafarkin maida yammancin Yerushelima babbar birnin kasar da za su kafa,suka toshe duk wata alakar da ke takanin su da Amurka,wadda ta dade tana taka rawa a rikicin Falasdinu a matsayin mai shiga tsakani.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2018-05-02 — 5:56 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme