MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KASANCEWAR BUHARI SHUGABAN KASA BAMU AMFANA DA KOMAI BA-Inji Sarkin Daura

       Zaman Buhari Shugaban Kasa Bamu Amfana Da Mulkin Sa Ba- Sarkin Daura

Mai marataba sarkin Daura, Dr. Umar Faruq Umar, a ranan Litinin ya ce jama’arsa da mutanen Daura na cikin halin kunci duk da cewa dansu, shugaba Muhammadu Buhari, ne shugaban kasa. Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawo hankalin ministocin da suka amfana da matsayin da shugaba Muhammadu Buhari ya basu na su kawo agaji masarautar ta ayyuka da noma.

Sarkin ya yi jawabi ne lokacin da ya karbi bakuncin ministan noma da raya karaka, Dakta Audu Ogbeh, wanda ya kai ziyarar ban girma fadar sarkin a garin Daura,yace ministocin da shugaba Buhari ya nada basu komai wajen taimakawa mahaifarsa Daura da ayyuka.

A jawabinsa yace: “Buhari yadda ka’idarsa ba zai kawo ayyuka Daura ba. Amma ministocinsa da suka amfana da matsayin da ya basu, su gode masa wajen kawo ayyukan cigaba Daura, mahaifarsa.” “Wannan jan hankali ne ga ministocin su sanya cikin kasafin kudinsu abubuwan da Daura za ta amfana da shi a gwamnatin Buhari.

“Idan ministocin suka ki kawo ayyuka Daura, sun yaudari shugaban kasa da mutanen Daura.”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-07 — 5:21 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme