MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARSHEN ZANCE: RAHAMA SADAU TA BAYYANA SAURAYIN DA TAKE MURADIN AURE-Karanta Kaji

Soyayya Gamon Jini: Rahama Sadau Ta Bayyana Saurayin Da Take Muradi

Fitacciyar tauraruwar fina finan Hausa, wato Kannywood, Rahama Sadau ta fito fili ta bayyana ma Duniya saurayin da take muradin soyayya da shi, kamar yadda HausaTop ta gano.

    
Rahama ta bayyana haka ne a shafinta na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda tace a kullum tana da muradin soyayya da wannan saurayi, wato ta mika masa kokon barar soyayya kenan.

Wannan kyakkyawan saurayi da Rahama ta mutun mawa kuwa shi ne, Alexx Ekubo, fitaccen jarumin fina finan turanci, wanda aka fi sani da suna Nollywood, haka zalika jarumi Alex ta kasance tsohon dalibin kwalejin tarayya ta garin Daura, FGC Daura.

Bugu da kari rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka Rahama Sadau ta na cikin wani Fim na turanci da ake shiryawa a yanzu haka, wanda ya kunshi Alex Ekubo, Ali Nuhu da sauran taurari
Daga @Hausaloaded. Com

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-02-01 — 3:09 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme