MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARO DA ALJANI: Aljihun Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kuka Kawowa Yanzu Ya Kashe Naira Miliyan 200 Don Gwabzawa Da Buhari A Zaben 2019-Karanta Kaji

Aljihun Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kuka Kawowa Yanzu Ya Kashe Naira Miliyan 200 Don Gwabzawa Da Buhari A Zaben 2019-Karanta Kaji

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Mun samu labari daga Jaridar The Cable cewa Kingsley Mogahalu wanda yana cikin masu harin kujerar shugaban kasa a zaben bana na 2019 ya kashe akalla Naira Miliyan 200 kawo yanzu wajen neman takara.

Kingsley Moghalu, wanda ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta YPP yace ya batar da abin da ya haura Naira miliyan 200 daga aljihun sa.

Moghalu ya bayyyana wannan ne lokacin da ya zauna da jama’a a wata hira da NTA jiya. ‘Dan takarar ya bayyana cewa bai da wani uban gida da ya tsaya masa, don haka da kudin sa yake amfani wajen neman takarar shugaban kasa, sannan kuma ya bayyana cewa zai samu sauran kudin kamfe ne daga masu bada gudumuwa.

Moghalu ya nuna cewa idan har yayi nasarar zama shugaban kasa a 2019, zai habaka tattalin arzikin Najeriya ta hanyar tallafawa kananan sana’o’i da. Moghalu yace a matsayin sa na mai ilmi, zai yi kokarin ganin ya gyara kasar nan.

Tsohon mataimakin gwamnan na babban bankin CBN, bako ne a harkar siyasa, sai dai yayi alkawarin cewa kudin da aka warewa tsare-tsaren da ke taba rayuwar talaka irin su N-Power za su isa ga wadanda ke bukata idan ya kafa gwamnati.

Gidan talabijin na NTA ne su ka shirya wannan shiri da taimakon hukumar nan ta Daria Media da kuma gidauniyar nan na MacArthur Foundation. ‘Dan takarar yayi magana na kusan sa’a 2 a gaban Duniya.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-10 — 9:42 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme