MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI:MUSABBABIN ABINDA DAKE FARUWA A KASAR BURMA TSAKANIN MABIYA ADDININ BUDDHA DA MUSULMAI KASHI NA 1

Cin Zarafin bil-adama: Kisan kare dangi da limaman addinin Buddha ke yi wa musulmi a kasar Burma kashi na daya.

Sabbin hotuna masu tayar da hankali dake fitowa daga kasar Myanmar, wato Burma, kasa mai makwabtaka da Indiya da China, masu daga hankali, kisan gilla kan yara kanana, mata da gajiyayyu, tsoffin da samari, duk don kokarin masu bin addinin bautar Buddha na su karar da kabilar Rohingya ta Musulmai, wadanda suka zo daga Bangladesh zamunna da suka wuce.

Kasar Myanmar, da a ka fi sani da Burma a da, ta na yankin kudu maso gabashin Asiya ne.

Kasar na da mutum kimanin miliyan 51 da kabilu a kalla 100 sannan ta yi iyaka da kasashen China, Bangladesh, Taiwan, da Laos. Mafi yawan ‘yan kasar mabiya addinin Buddha ne sai kuma musulmi ‘yan kabilar Roghingya da ba su wuce kaso 10 ba na mutanen kasar da ke wata jiha mai suna Rakhine da ke kusa da iyakar kasar ta Burma da Bangladesh.

Rahotonni daga kasar ta Burma sun dade suna kyara yadda tsirarin musulmin kasar ke fuskantar muzanta da kisa daga mabiya addinan Buddha da gwamnatin kasar ke goyawa baya.

Wani rahoto da musulmi ke yadawa a kafafen sada zumunta na zamani na nuni da cewar tun bayan yakin duniya na biyu musulmin kasar Burma ke cikin halin muzgunawa har yanzu amma kasashen duniya sun nuna halin ko in kula tare da zargin kafafen yada labarai da kin yayata halin da musulmin kasar ke ciki.

Hotuna dai na kisan gilla, gawarwaki da suka hada da yara sun cika shafukan sada zumunta, sarai kuma gwamnatin kasar tayi mursisi taki daukar mataki, wai duka labaran na karya ne, har ma masu gudun hijira sun kusa kai miliyan daya.

Musulmin sun ce tun a shekarar 1784 wani Sarki, mai suna Bodawpaya, mabiyin addinin budda ya yi kokarin hallaka duk musulmin kasar bayan ganin yaduwar da addinin musuluncin ke yi a yankin kasar.

Yanzu dai manyan muryoyin shugabannin duniya musamman shugaban jam’iyyar Leba ta Ingila, Jeremy Corbyn, Ministan waje na Birtaniyar Boris N. da ma ‘yar kiran kare hakkin mata da yara Malala Yusufzai sun zafafa kausasan sukar da kasar ke sha.

An kuma bude shafin korafi a Change.Org, wanda har ya kai sa hannun mutane kusan 300,00, duk domin matsin lamba ga gwamnati ta dau mataki, ko majalisar dinkin duniya ta shiga rikicin. Kuma zaku iya latsa wannan botir domin kawo wa jama’ar Rohingya dauki da muryar ku. https://www.change.org/p/jeremy-corbyn-mp-take-aung-san-suu-kyi-to-international-court-of-justice-over-ethnic-cleansing-of-rohingya

(Visited 1 times, 1 visits today)
Updated: 2017-09-06 — 3:38 pm

1 Comment

Add a Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme