MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI:Fim Din Yaki A Soyayya Ya Shiga Sahun Manyan Fina Finai 20 A Nijeriya

                           Fim Din Yaki A Soyayya Ya Shiga Sahun Manyan Fina Finai 20 A Nijeriya

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shahararren fim din na kannywood maisuna Yaki A Soyayya wanda jaruma Nafisa Abdullahi ta shirya ya shiga rukunin manyan fina finan 20 da ake ji dasu a Nijeriya.

Fim din Yaki A Soyayya shine na 17 cikin fina finai 20 da aka haska a sinima a fadin kasar daga ranar 28 ga watan Disamban 2018 zuwa ranar 3 ga watan Janairu na wannan shekarar 2019.

Kungiyar sinima na Nijeruya wato Cinema Exhibitors Association Of Nigeria (CFAN) ce ta saki jerin fina finan a shafinta na twitter a ranar laraba,9 ga watan Janairu.

Kungiyar tayi bayanin  cewa jerin fina finan na daidai da bayyana yadda fina finan sukayi fice a kullum a sinimomin Nijeriya.

Daga jerin fina finan fim din Yaki A Soyayya ya samu Naira N722,000 a karshen mako sannan kimanin Naira Miliyan N1,276,000 cikin kwanaki bakwai kacal.

Da take martani wadda ta shirya fim din Yaki A Soyayya Nafisa Abdullahi tace tayi matukar farinciki da fim dinta ya shiga jerin manyan fina finai 20 a fadin Nijeriya baki daya.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-11 — 12:25 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme