MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Yadda Wani Magidanci Ya Saki Matarsa Saboda Ta Zabi Buhari

                                 Miji Ya Saki Matarsa Don Za Ta Zabi Buhari

Abdullahi ya shaida wa manema labarai cewa ya yi wa matarsa Hafsat Suleiman saki biyu ne bayan da ta sha alwashin cewa “ita Shugaba Muhammadu Buhari za ta zaba a zaben 2019.”

Ya ce har sai da maganar ta kai gaban iyayenta, inda daga nan ne sai ya yanke hukuncin sakinta wanda kuma “har ya balla mata hakori,” a cewarsa.

Amma mun yi magana da yayanta mai suna Ibrahim Suleiman, wanda ya bayyana bacin ransa game da abin da ya faru. Kuma ya sha alwashin cewa “ba za ta koma dakinta ba.”

Da alama zaben 2019 zai fi wadanda suka gabace shi ta fuskar rabuwar kawunan al’umma da ke mara wa mabambantan ‘yan takara baya.

Wasu masu sharhi kan al’amura a kasar suna ganin hakan bai rasa nasaba da yadda duka manyan ‘yan takarar biyu suka fito daga yanki guda – wato arewacin kasar kuma dukkannsu Musulmi.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-24 — 11:20 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme