MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Yadda Soyayya Mai Karfi Ke Shirin Kulluwa Tsakanin Jaruman Kannywood 2 Adam Zango Da Fati Washa

Dandalin Kannywood: Ana zargin soyayya mai karfi a tsakanin Adam Zango da Fati Washa

Kamar yadda maganganun¬† keta yawo a bakunan jama’a dai yanzu shine irin so da kauna mai karfin gaske da ake zargin ya shiga tsakanin fitattun jaruman nan na wasan Hausa fim a masana’antar Kannywood watau Adam Zango da Fati Washa.

Wannan dai na zuwa ne lokacin da hotunan jaruman biyu a tare cikin raha da daman gaske ke cigaba da bayyana a kafafen sada zumunta na zamani inda kasafai ake ganin su suna ta raha suna dariya.

Majiyar Dandalin Mujallarmu ta samu cewa masu sharhi akan al’amurran yau da kullum a masana’antar shiya fina-finan ta Kannywood sun lura da cewa yanzu fina-finan da jaruman biyu keyi a tare na ta kara yawa a kasuwanni.

Sai dai kuma duk da maganganun dake ta yawo a kan lamarin, har yanzu jaruman sun ki fito su tabbatar ko kuma su karyata batun wanda hakan ke kara darsa kokwanto a zukatan masu sha’awar fina-finan.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-13 — 11:12 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme