MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Yadda Marigayi Shehu Shagari Ya Sauke Alqur’ani Mai Tsarki Sau 156 daga 1988 zuwa 2009-Duba Hoto

      Marigayi Shehu Shagari ya sauke alqur’ani sau 156 daga 1988 – 2009

Sabbin bayanai sun soma bayyana na irin kusancin tsohon shugaban kasar Najeriya, Marigayi Shehu Shagari ga Allah da kuma irin rikon da ya killace kansa ya shagaltu da ibadar Allah a shekarun baya-baya na rayuwar sa.

A wani dogon rubutu da wani daya daga cikin dangin Marigayi Shagari yayi a dandalin sadarwar zamani mai suna Salisu Usman, yace tsohon shugaban kasar ya sauke Al-qur’ani mai girma akalla sau 156 daga shekarar 1988 zuwa 2009.

Dandalin Mujallarmu ta samu cewa an dai ga wannan ne a cikin ajiyar da tsohon shugaban kasar yayi a dakin sa inda aka ga wata takarda da yake rubuta duk ranar da ya kammala saukar alqur’ani.

Ga dai rubutun da shie Salisu Usman din yayi nan kasa: 

ALLAH KE SO A SANI YANZU – Ya SAUKE ALKUR’ANI SAU 156

Tun bayan da aka sauke shi a kan mulki kuma ya kwashe kusan shekara biyu a tsare wanda ko hasken rana ba a bashi damar ya gani ba.

Yau na ci karo da abin mamaki ga marigayi Shehu Shagari (Allah Ya gafarta masa) cikin turakarsa aka binciko wadansu takardu da suke kunshe da yawan adadin saukar Alkur’ani Mai Girma da yayi wanda tsakanin sa da Allah sai iyalansa suka sani sai mu kuma yau da muka gani.

Na irga abinda idona zai iya gani a takarda guda biyu kawai sai naga daga 1988 zuwa 2009 ya sauke Alkur’ani sau 156. Wannan ba karamin nasara bace ace mutum ya samu matsayi irin nasa amma bai manta da ubangijinsa ba.

Wanda yayi don Allah Ya huta.
Wurin Allah can ya huta.
Babu kulli ko na buta.
Hakan Allah ya nufa ga shehu

Kun kasa daura sharri gare shi
Tunda Allah ya san abin shi
Ya tsare shi kab gare shi
Tunda ya mutu bai wulakanta ba.

In fa Allah ya sowa bawa
Babu kulli ko yin dagawa
Ba wanda zai kai shi daukakawa
Gun mutane har da masu so ya kasa.

Yau kai ake son aji ka
gashi jalla ya dauke ranka
babu jinin wani ko wanin ka
gashi yau duk sun dimauta

Shifa zalunci bashi dogewa
A wurin shugaba ko dadewa
Tun farin safiya dake budewa
Jalla zai hukunta masu daddannewa

Jalla ya bar fir’auna akan fa mulki
Yai duk abin da yake gani da kulki
Ya kashe ya tsare don yana da walki
Hakan bai hana Allah kama shi ba.

Hakan Allah ya bar irin su
Hamana can da abokanen su
Irin su Walidu da yan uwansu
Ranar badar Allah ya ida nufinsa

Yawan suka da aki a kanka
Hakan Allahu ya rubuta maka
Yau gashi duk ana ta yabonka
Hakan Allahu ya kaddara maka

Yau da gobe tana hannunsa
Wanda ya hadaku da Dasukinsa
Ga Malam Gumi da a yarintarsa
Abota ta Allah ba ta shirme ba.

Rayuwaku akwai abin fahimta
Hakuri da juriya da aminta
Ga yawan ibadar har da kyauta
Allahu ya hadaku cikin salama

Na yi kuka yau akai na
Da irin masu karanci shekaru na
Mun rasa shugaba mai amana
Shagari Allah Ya gafarta.

Yawan karanta abin karantawa
Mai yawan ladan harrafunwa
Goma bisa goma na alkawartawa
Yaba ka da kari fin isarka.

Allah Ya yiwa Annabi Salati
Da aminci da yarda masu kunuti
Sahabbai da mabiyan Salati
Irin na Allah mai yawan bayarwa.

Salisu Hassan Webmaster
08038892030
08/01/2019

                                      

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-11 — 1:22 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme