MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Yadda Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Caccaki Wata budurwa Dake Kokarin Kwacen Saurayi

Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Caccaki Wata Budurwa Dake Yunkurin Kwacen Saurayi-Karanta Kaji

Tauraruwa fina finan hausa Nafisa Abdullahi ta caccaki wata data zarga da yunkurin kwacen saurayi duk da yangar da take yiwa maza

Nafisa ta saka wani sako a shafinta na Tuwaita inda ta rubuta cewa…

“Kina ta wani yanga amma kin koma gefe kina kokarin yiwa kawarki kwacen saurayi,kina rokon abubuwan da kike nunawa duniya cewa kinfi karfinsu,kina yanga kamar ke wata ce,yanzu kallon huhun ma’ahu nike mike,ba kima sai kokarin kai kanki inda Allah bai kai kiba.”

Nafisa dai bata bayyana ko da wa take ba,amma masoyanta da dama sun rika bata baki a shafin nata yayin da wasu suka rika tambayar wa ya tabota?

Abin tambaya anan shine nata saurayin ake shirin kwacewa ko kuwa shiga fadanĀ  wata tayi?in dai tayi tsami zamu ji.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-02-02 — 9:50 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme