MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: YADDA BUDURWAR WANI SOJA TA AURE WANI SAURAYI BAYAN AN TURA SHI BORNO

Ba Zato Ba Tsammani Naci Karo Da Hotunan Matar Da Zan Aura A Social Media Ta Aure Wani-Inji Wani Soja

Wani sojan Najeriya da ke filin daga a yankin Arewa maso gabashin Najeriya bayar da labarin yadda ya gano Budurwarsa da ya bari a gida tayi aure ba tare da ya sani ba kwatsam sai dai ya ga hotunan aure a shafunkan sada zumunta.

Wani sojan Najeriya mai suna Emmy Benison ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta inda ya bayar da labarin yadda budurwarsa da suka kwashe shekaru hudu suna soyaya tayi aure ba tare da ya sani ba.

Benson ya ce sun kwashe shekaru biyu ba su hadu ba amma yana sa ran da zarar ya dawo ya garzaya wajen ta domin su cigaba da soyaya kamar yadda suka dade suna yi.

Sai dai ya yi matukar mamakin ganin hotunan auren da wani mutum ba tare da ta sanar dashi cewa za tayi aure ba. A cewarsa, ya yi kuka amma dole ya jajirce ya cigaba da aikinsa saboda babu damar karayar zuciya a filin daga.

Ga sakon da ya rubuta a shafinsa na Instagram: ‘Mun fara soyaya shekaru hudu da suka wuce amma nayi shekaru biyu ban dawo gida ba. Bata fada min cewa ba zata iya jira na ba. Fata ne shine wata rana zan dawo gida kuma in faranta mata rai amma yau kwatsam sai na farka naga hotunan auren ta.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-07 — 9:16 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme