MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: WASU SANATOCI NA YUNKURIN TSIGE SHUGABA BUHARI-Inji Tinubu

                          Ana kulla tuggun tsige shugaba Buhari – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya yi zargin cewar wasu mambobin majalisar dattijai na yunkurin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tinubu ya gargadi masu yunkurin dasu gaggauta ajiye wannan kudiri nasu domin ba zai taba samun karbuwa ba tare da kwatanta yunkurin nasu da cewar “tamkar kadangare ne yake kokarin yin kokawa da jimina.” Wadannan kalamai na fitowa daga bakin Tinubu ne yayin da yake gabatar da jawabi ga dandazon jama’ar da suka halarci bikin karbar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, biyon bayan canjin shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.

Buhari da Tinubu “Mu muna gwamnati ne don jama’a ba don kudi ko son mulki ba. Wannan shine banbancin mu da jam’iyyar PDP da suka yarda ceware ana neman mulki ne domin tara abin duniya da kuma nuna isa,” a kalamana Tinubu. Sannan ya cigaba da cewa, “shekara 16 ‘yan Najeriya suka bawa jam’iyyar PDP amma sun kasa kawo canji a rayuwar mutane, sun mayar da hankali ne kawai wajen wawura, handama da babakere a kan dukiyar kasa.”

Akazalika, Tinubu, ya nuna farincikinsa da dawowar Akpabio cikin jam’iyyar APC tare da mika godiya ta musamman ga matarsa, Ekaete Akpabio, bisa goyon bayan da take bawa mijin nata.

A nasa jawabin, Boss Gida Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya kuma mutumin da ya wakilci mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sanar da jama’ar jihar Akwa Ibom cewar shugaba Buhari na kaunar su kamar yadda yake kaunar dukkan ‘yan Najeriya.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-09 — 1:30 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme