MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: WANI SAURAYI YA KASHE KAN SA SABODA BUDURWA SA TAKI AMINCEWA DA BUKATAR SA

         Wani Matashi ya kashe kansa bayan Budurwar sa ta ƙi amintuwa da buƙatar sa

Labaran duniya Mun samu rahoton cewa wani matashi can kasar Zimbabwe, Shupikai Chikuvira dan shekara 29 a duniya, ya kashe kansa bayan da budurwar sa ta hau kujerar na ƙi kan buƙatar sa ta guduwa tare da shi domin cikar burin su na auren juna.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, wasu kauyawa sun yi kacibus da gawar wannan matashi a garin Mutawatawa inda cikin gaggawa suka ankarar da jami’an hukumar ‘yan sanda.

Kakakin hukumar ‘yan sanda na yankin Gabashin garin Mashonaland, Sufeto Tendai Mwanza, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda jaridar Bulawayo 24 ta kasar ta ruwaito. Wani Matashi ya kashe kansa bayan Budurwar sa ta ƙi amintuwa da buƙatar sa

Dandalin Mujallarmu ta fahimci cewa, wannan matashi ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a ranar 4 ga watan Agusta bayan wata sa’insa da ta shiga tsakanin sa da abar kaunar sa.

Sanadiyar sa’insar dai ba ta wuci rashin amincewa da buƙatar sa ta guduwa tare da shi domin su auri junan, inda ta ce hakan ba zai yiwu sakamakon rashin samun albarka daga bangaren iyayen ta.

Rahotanni sun bayyana cewa, Chikuvira dai ya ƙarƙare zancen sa da sahibar sa kan cewa zai kashe kansa, tun da dai ta ƙi amincewa da buƙatar sa da sai gawar sa aka tsinto ta na reto jikin wata itaciya.

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2018-08-09 — 1:21 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme