MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: WANI BAFULATANI YA KASHE KANSA BAYAN MUTUWAR SHANUN SA GUDA 200

Ya kashe kan sa bayan mutuwar shanun sa fiye da 200.

Wani bafulatani makiyayin dabbobi maisuna Muhammad Abdulkadir mai kimanin shakaru 56,yayi kukan kura cikin tekun benuwe a karamar hukumar logo dake jihar lagos,bayan mutuwar shanun sa kwara 200 sanadiyyar kishin da yunwa data addabe su.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya a jihar Benuwe, Garus Gololo, ya tabbatarwa da jaridar Punch cewar marigayin ya kashe kan sa ne bayan yunwa ta hallaka shanun sa 200.

Ya kashe kan sa bayan mutuwar shanun sa fiye da 200 Ya kashe kan sa bayan mutuwar shanun sa fiye da 200 Ranar 1 ga watan Nuwamba nan da muke ciki ne gwamnatin jihar Benuwe ta haramtawa makiyaya yin kiwo dazukan jihar, dalilin da yasa Fulani makiyaya hijira zuwa makobtan jihohi.
Kungiyar Fulani makiyaya ta bayyana cewar wannan doka ta gwamnatin jihar Benuwe ta jawo asarar shanu fiye 600 saboda rashin abinci da ruwa. Gololo ya nuna takaicin sa bisa mutuwar Abdulkadire, uban yara 22, saboda rasa shanun sa 200 daga karancin abinci da ruwa.
“Ya kashe kan sa saboda ganin yadda yunwa ta dinga yi wa shanun sa dauki dai-dai yayin da yake kokarin kora shanun domin fita daga jihar ya zuwa inda shanun zasu samu abinci da ruwa”.
Inji shugaban kungiyar Fulani makiyaya a jihar Benuwe. Gololo ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo ma su agaji kafin duk dukiyar su ta balbalce saboda dokar da gwamnatin jihar Benuwe ta kakaba ma su.
Da aka tuntubi kakakin hukumar’yan sanda a jihar Benuwe, Moses Yamu, ya ce ba a kawo ma su rahoton afkuwar mutuwar ba.

 

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Shafin Facebook
Shafin Twitter
Shafin Instagram
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: [email protected]

Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa


Shiga Mujallarmu YouTube channel kayi subscribe domin kallon bidiyo da muka tanadar maka don nishadi da ilimantarwa
Updated: 2017-11-12 — 2:44 pm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme