MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Wah Bashir Chiroki Ya Taimaka Lokacin Da Tauraruwarsa Ke Haskawa A Kannywood-Inji Ali Nuhu

Babu Wani Dake Kannywoood Da Zai Taimakawa Chiroki Sai Idan Yadawo Masana’antar Ya Sasanta Da Masu Shirya Fina Finai-Inji Ali Nuhu

Ali Nuhu ya kalubalanci wani ma amfani da shafin twitter cewa ya bayyana masa mutanen da abokin sana’arsa Bashir Bala,wanda akafi sani da Chiroki ya tallafawa lokacin da tauraruwarsa ke haskawa a fagen wasan kwaikwayo.

Sai dai mutumin,wanda ke amfani da sunan Doctor Kiyawa,ya nuna rashin jindadin ne kan yadda yace jaruman kannywood sunyi watsi da Chiroki duk da cewa yana bukatar taimako.

A wata hira da gidan talavijin na arewa 24,chiroki yayi ikirarin cewa masu shirya fina finai da jaruman kannywood sun daina sanya shi a fim,shiyasa yanzu yake saida kunun aya.

Doctor Kiyawa yayi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin guda suyi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar basa samun komai.

A kannywood ne zaka ga mace ta shigo fim wanann shekarar amma tafi wanda yayi shekara 10 yana sana’ar fim kudi,Ali Nuhu kai ne wanda yanzu jama’a suke gani da kima a kannywood don ku yiwa Chiroki wani abu wanda shima bazai manta cewa kunyi masa halacci ba.

Sai dai jerin martanin da Ali Nuhu yayiwa masu irin wannan korafi,ya kalubalance su dasu nuna masa irin taimakon da Chiroki ya baiwa Kannywood.

Zan iya maka tambaya,lokacin da Chiroki yake tashe waya taimakawa?maimakon haka akan kudi menene baya yiwa masu shirya fim? Yakamata musan abin mukeyi.

Yace bai kamata a rika yiwa kannywood rashin adalci ba.wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu.

Jarumin yace babu wani dake kannywood da zai taimakawa Chiroki,yana mai cewa “yakamata ya dawo masana’antar ya sasanta da masu shirya fina finai,sannan ya cigaba da aiki kawai.”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-24 — 11:38 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme