MUJALLARMU

...ILIMANTAR DA AL'UMMAR MU

KARANTA KAJI: Tarin Garabasar Dake Tatttare Da Auren Matan Kannywood-Inji Jaruma Ladidi Tubless

           Akwai dadi: Ladidi ‘Tubeless’ ta yi kira ga maza su rika auren ‘yan fim

Daya daga cikin fitattun jaruman nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood mai fitowa a matsayin uwa wadda Ladidi Abdullahi amma wadda aka fi sani da Ladidi Tube less ta yi ikirarin cewa duk duniya babbu mace mai dadin aure kamar ‘yar fim.

Ladidi ta kara da cewa ita ‘yar fim saboda irin yadda take taka rawa a cikin fina-finai, tana kara ilimin zamantakewa irin ta aure sosai a don haka ne ma take kira ga maza su rika auren ‘yan fim din.

Hajiya Ladidi kamar dai yadda muka samu ta yi wannan ikirarin ne a yayin wata fira da ta gudanar da wakilin majiyar mu a garin Kaduna dake zaman mahaifar ta.

Dandalin Mujallarmu ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa abun takaici ne yadda mutane ke yi wa ‘yan matan fim din mummunar fahimta musamman ma yadda su ke gudun auren su alhali kuma sun fi kowa dadin aure.

Haka ma dai jarumar da aka bukaci ta bayar da shawara zuwa ga sauran matan da ke harkar fim din sai ta ce “Shawara ta gare su shi ne su yi karatu, saboda na ga gaba abubuwa za su canje wanda zai kai lokaci da sai kana da karatu za ka yi shi kansa fim din ma.”

Danna nan idan kana neman BIDIYON HAUSA masu ilimantar wa da NIshadantarwa musamman na Zamantakewa tsaknin Ma'aurata:


Domin Kallon Videos namu masu Kayatarwa

Updated: 2019-01-26 — 11:02 am

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MUJALLARMU © 2017 Frontier Theme