KARANTA KAJI: TARIHIN WANI MUTUM MAISUNA ABBA DAYA SHARE SHEKARU 40 YANA RAYUWA DA KURA ACIKIN DAKI DAYA

Na Share Kimanin Shekaru 40 Ina Rayuwa Da Kura Acikin Daki Daya-Inji Abba.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kamar yadda kowa ya sani kura dai tana daya daga cikin manyan dabbobin daji masu hadarin gaske,sai kuma gashi a wani karamin gari a kasar Ehiopia an samu wani mutum maisuna Abba ya share kimanin shekaru 40 tare da kura zaune a gida daya.

Kamar yadda majiyarmu ta Dandalin Mujallarmu,keda labari Abba yace akoda yaushe shi yake baiwa wannan kura abinci tsawon wadannan shekaru,amma babu wata cutarwa a tsakanin sa da ita.

Abba ya kara da cewa bai taba sanyawa kurar tukunkumi ba abaki,ko killace ta a kije saboda gudun kada ta cutar dashi.

Kowa dai yasan kura batada hakuri a daji balle acikin gari inda take ganin mutune akoda yaushe,dalilin haka yasa wasu mutane suke cike da mamakin yadda alakar Abba da wannan kura ya dore kimanin shekaru 40 batare da ta cutar dashi ko sau daya ba.

Bugu da kari wannan mutum Abba yace shi da wanna kura tamkar abokai ne,don kuwa dukkan abinda yaci to sai ya bata sannan kuma bai taba sanyawa aransa cewa zata cutar dashi ba watarana.

This website uses cookies.